Mon. Mar 31st, 2025

Zan Cigaba Da Ba Da Gudunmuwa Ga Firamaren Ƙofar Nasarawa -Shugaban Jami’ar Capital City

By Saleh Aliyu Dec 27, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Dakta Abdulmalik Isa Abdullahi Ɗan’Iyan Okene, ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da Jami’a mai zaman Kanta ta Capital City da ke Kano, ɗaya daga tsofaffin ɗaliban makarantar Firamare ta ƙofar Nasarawa aji na 1981.

Ya ce dukkan ‘yan gidansu a lokacinsa suke unguwar Yakasai makarantar ta ƙofar Nasarawa Firamare suka yi, kuma ga shi sun yi taro na tsaffin ɗalibai waɗanda aka shafe shekaru 40 ba a haɗu ba, Allah ya haɗa su, wasu dama ana haɗuwa, akwai ma waɗanda suka yi makarantar ya ɗauke su aiki a kamfani suna aiki.

Ya ce taron nasu na tsofaffin ɗaliban ya nuna makarantar mai albarka ce. Duk ƙoƙarin da za su yi wajen dafa mata za su yi. Kuma akwai mutane da ya gani sai a nan suka haɗu bayan tsawon lokaci da suka gama makarantar. Ya ji daɗin hakan.

Ya ce shi zumunci abu ne mai dadi da alkahiri a ciki, kuma wannan haɗuwa zai ɗorar da zumunci a tsakaninsu da daɗa ƙarfafa shi a tsakaninsu.

Ya ce ko da aka gaya masa taron ya bayar da gudunmuwa, kuma za su cigaba da bayarwa, domin ya ga makaranta tana da buƙatar gyara. Zai nemi wani ɓangare ya dauka ma ya yi gyaran.

Ɗan’iyan Okene, Dakta Alhaji Abdulmalik Isah Abdullahi, ya yi nuni da cewa duk abin da mutum ya zama yau makarantar ce ginshiƙi shi, ya sa yau daga Firamare ya gina Jami’a ta kansa, kuma cikin godiyar Allah ya zama dole ya bai wa makarantar gudunmuwa.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *