Daga Zubairu Lawal
Sabon Shugaban Kungiyar ALGON ta kasa Hon. Bello Lawal yayi alkawarin yin aiki kafada da kafada da Gwamnatin tarayya dana jihahohi .
Sabon Shugaban yayi kira ga Shugabannin kananan hukumomi da su zage dantse wajen samar da cigaban kananan hukumomi.
Hon. Bello Lawal yace; wannan cin gashin kai da Gwamnatin tarayya ta basu, ana bukatar suyi amfani da dukiyar wajen gina kasa.
Yace; samar da tsaro da noma da kiwon lafiya da gina hanyoyin karkara da bunkaa matasa.
Yace; bazasu zura ido su kyale duk Shugaban da zaiyi almundahana ba.
Sabon Shugaban ya yabawa Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu. Ya kuma ce zasuyi aiki kafada da kafada tsakanin Qananan hukumomi da Jihohi da tarayya.
Hon. Bello Lawal yayi godiya ga tsohon Shugaban ALGON ta kasa wanda ya sauka. Hon. Aminu Ma’azu Maifata. Yace zai daura salon mulkinsa daga Inda ya gada. Domin da damansu sun yaba da cigaban da Aminu Mu’azu Maifata ya kawowa Kungiyar ALGON a lokacinsa.
Sabon Shugaban ya bayyana hakane bayan rantsar da su.
Shima tsohon Shugaban ALGON da ya sauka. Alhaji Aminu Ma’azu Maifata tsohon Shugaban Karamar hukumar Lafia, yayi godiya ga Allah da ya nufeshi da kammala wa’adinsa lafiya.
Ya kuma godewa membobim Kungiyar saboda yadda suke masa godiya saboda hadin kai da cigaban da aka samu a lokcin mulkinsa.
Hon. Maifata yace; har yanzu sunanan zasu cigaba da bada shawarwari ga Kungiyar.
Membobin Kungiyar ALGON ta kasa ta gudanar da zaben sabbin Shugabanninta ranar Talata 8//2024 a garin Lafia fadar Gwamnatin jihar Nasarawa.
Zaben ya gudana ne bayan karewar wa’adin Tsohon Shugabanta Alhaji Aminu Ma’azu maifata Shugaban Qaramar hukumar Lafia.
An zabe Hon. Bello Lawal Shugaban karamar Hukumar Kaita ALGON na jihar Katsina a matsayin sabon ALGON na kasa
Algon na jihar Jigawa Hon. Bala Usman kiyawa Ya zabe shi a matsayin sabon Shugaba inda ya samu goyon bayan takwararsa Algon na jihar Enugu Hon. Okechikuw Edeh
An kuma zabe sauran Shugabannin da zasu cigaba da jan ragamar Kungiyar tare.