Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Abdullahi Muhammad Bala ‘Yan’leman na ɗaya daga cikin masu neman takarar shugabancin ƙungiyar ‘yan kasuwar Ƙofar Ruwa, Kanao, ya bayyana dalilin fitowar sa takarar da cewa saboda ganin abubuwa daban-daban da ke faruwa a kasuwar na rashin ci gaba da koma baya da take fuskanta ta sa ya fito.
Ya ce takarar da ya fito ba na yin kansa ba ne. Dattawan kasuwa da matasa da sauran masu kishi da son ci gaban kasuwar ne suka ga dacewar ya ba da gudunmuwa, ganin jajircewa da yake a kan ci gaban kasuwar. Zai ba da gudunmuwa sosai idan ya zama shugaba.
Alhaji Abdullahi ‘Yan’leman ya shaida wa ‘yan jarida cewa, “Akwai matsaloli da suke damun kasuwar da yawa, musamman ɓangaren harkar tsaro ta addabi kasuwar matuƙa, domin sai ka rufe shago ka tafi gida ka dawo da safe ka ga an ɓalle maka wani lokacin har fasa bango ake a shiga a kwashe musu kaya,” in ji shi.
Ya ce yana daga babban burinsa ya kyautata tsaron kasuwa da alaƙa da gwamnatin jihar Kano domin a zo a riƙa yi musu ayyuka na ci gaba, kama daga gyaran hanyoyi da kuma samar musu da rijiyoyin burtsatse da kuma sanya musu fitilu da za su haskaka kasuwar su taimaka wajen inganta tsaro.
‘Yan’leman ya yi nuni da cewa ƙungiyar tasu ta yi shugabanni da yawa tun daga kan Alhaji Mati da Alhaji Tukur, wanda daga kansa shugabanni da suka biyo baya babu abin da suka kawo wa kasuwar na ci gaba.
Ya ce, “Komai ka gani ya gyaru ko ya lalace a gida daga mai gida ne. Yanzu muna duba yaya za a yi mu zo mu haɗa kai don gyara kasuwar, domin kasuwa ce mai albarka da daraja da ko da sukurdireba ka zo za ka sami abin da za ka ci abinci da kai da iyalinka ballanta ma kana da abin yi, ba kamar sauran kasuwanni ba,” ya jaddada.
Ya ƙara da cewa kasuwa ce mai tarin matasa da ɗimbin albarka, amma shugabanni da suka gabata da ba su da manufofi masu kyau, amma su sun shigo da manufofi masu kyau na neman wannan takara in suka yi nasara za su yi abin da za su bar tarihi ta inganta ta da kawo mata ci gaba.
Alhaji Abdullahi Muhammad ‘Yanleman ya ce akwai shugabanni na siyasa musamman a tsarin wannan gwamnati ta jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf da suke so su kawo wa kasuwanni gudunmuwa na haɓaka su idan ba a sami shugabanni da za su ba da himma a kasuwar tasu ba, wannan alkairan ba za su zo musu ba.
Don haka burinsa idan ya yi nasara za su kawo ci gaba sosai ta haɗa kan kowa, domin kasuwa ce da take da mutane mabambanta da suke zuwa daga sassan ƙasar nan har da ƙasashen ƙetare. Za su ƙulla alaƙa da gwamnati tun daga matakin ƙaramar hukuma da ta jiha da ta tarayya don ba su haɗin kai don ci gaban kasuwar.
Ya ce tun daga lokacin da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Dala Manuda Madakin Gini ya yi musu kwalta a wani titi na kasuwar da ‘yan ayyuka babu wani da ya sake zuwa ya yi musu wani abu, amma suna fata a wannan gwamnati tasu ta tafiyar Kwankwasiyya mai
albarka mai son ci gaban al’umma da take yin ayyuka nagari za su jawo hankalinsu su zo su yi musu ayyuka a kasuwar.
Abdullahi ‘Yan Leman ya ce suna da manufa da za su bayar da gudunmuwa sosai ga ci gaban kasuwar a fannoni da dama, musamman inganta tsaro da gyara hanyoyi da haɗa alaƙa da gwamnati domin ci gaba da bunƙasar kasuwar da ‘yan kasuwa da ke hada-hada na ciki da wajen ta.