Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana gwamnatin injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa mai son cigaban mata ce duba da irin kulawa da yake bai wa fannoni daban-daban.
Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.
Ya bayyana cikar Gwaman Abba Kabir Yusuf shekaru 62 a matsayin abin farin ciki ne ga matasa da duk al’ummar jihar Kano suna taya shi murna a kan wanan cigaba, da ya shigo da abubuwa na alherai a cikin wannan sabuwar shekara.
Ya ce idan aka duba kasafin kuɗi da Gwamna ya gabatar na shekaran nan kusan duk ya ba da muhimmanci ga tsare-tsaren matasa na ba su tallafi sa ba su horo a kan sana’o’i da bunƙasa ilimi su.
Hon. Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso Kwamishina da wasanni na jihar Kano ya ce, za su dage ba dare ba rana wajen riƙe amanar da Gwamna ya ɗora musu na bunƙasa cigaban matasan jihar Kano.