Tue. Apr 1st, 2025

Za Mu Cigaba Da Ƙarfafa Magajin Rafin Haɗejia Gwiwa Don Samun Nasara -Hajiya Amina Aliyu Babandede

By Saleh Aliyu Feb 10, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana Magajin Rafin Haɗejia da cewa mutum ne na mutane da ƙauna da soyayya ta sa aka zo daga sassa daban-daban domin taya shi murnar naɗin da aka yi masa.

Mai ɗakin Magajin Rafin Haɗejia, Hajiya Amina Aliyu Babandede ce ta bayyana haka ne da take hira da ‘yan jarida a yayin taron taya murna da walima da aka gudanar na naɗin ta ƙara da cewa shi mai gidan nata mutum ne na mutane da ba ya ƙyamar jama’a kowa nasa ne su al’umma shaida ne a kan haka.

Ta ce tabbas su a matsayinsu na iyalansa, masoyi ne shi, mai karamci a gare su, wannan rana ce da ba za su manta da ita ba tare da gode wa Allah da ya yi musu komai ba abin da za su ce sai ƙara taya shi da addu’a a kan Allah ya yi riƙo da hannunsa ya ba shi ikon zartar da aikin da yake kansa.

Hajiya Amina Aliyu Babandede ta ce za su cigaba da taya shi da addu’a da ƙarfafa masa gwiwa wajen aiwatar da ayyukansa kamar yadda suka saba, domin ganin ya cigaba na samun nasara.

Shi ma a nasa ɓangaren Maganin Rafin na Haɗejia Muhammad Babandede ya gode wa Sarkin Haɗejia, wanda ya ba shi dama ya naɗa shi sarautar Magajin Rafi, kuma Ɗan Majalisar Sarki dama akwai alaƙa sosai tsakaninsu da fadar Haɗejia tun kaka da kakanni.

Ya ce da yardar Allah zumunci da ke tsakaninsu da zai ɗore har ‘ya’ya da jikoki, kuma dama ita sarauta nauyi ne na kulawa ga al’umma da addini dama marigayi mahaifinsu shi ne shugaban marayu da masu rauni tsofaffi da mata da suka rasa mazajensu na jihar Jigawa a ƙungiyar Izala da yanzu shi aka ɗorawa wannan nauyi.

Sabon Magajin Rafin na Haɗejia Alhaji Muhammad Babandede ya ce aikin sarauta na taimaka wa al’umma ne kuma mahaifinsu marigayi ba shi da aiki da ya wuce taimakon al’umma don haka su ma za su cigaba da riƙe wannan nauyi da izinin Allah.

Shi ma a nasa ɓangaren tsohon shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa mai ritaya, Muhammad Babandede ya ce lokacinsa aka ba da wannan sarauta sun yi taro suka ce a bai wa ɗan’uwansa shi ya fi kowa dacewa da sarautar, kuma Sarki ya yarda ga shi yau an naɗa shi.

Alhaji Muhammad Babandede ya ce suna yi wa Sabon Magajin Rafin fatan alheri domin mutum ne da yana da nauyi da yawa a kansa, suna fata Allah ya ba shi ikon riƙe wannan nauyin. “Muna godiya ga Sarkin Haɗejia bisa soyayya da ƙauna da yake nuna mana,” in ji ta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *