Daga Ibrahim Muhammad
Hajiya Zainab Muhammad Sule Minjibir na daga cikin iyaye mata da ƙungiyar haɗin kan Minjibir da aka fi sani da Minjibir Solidarity Forum ta karrama a yayin taron da ta gudanar ranar Lahadin da ta gabata.
Da take zantawa da ‘yan jarida bayan karɓar lambar yabon, Hajya A’isha ta ce za ta ci gaba da ba da gudunmuwa kamar yadda ta saba domin bunƙasa yankin don kishin Minjibir tamkar a jininta yake.
Ta ƙara da cewa, “Idan aka ce Minjibir ji nake kamar ma ni kaɗai ce don haka ma a ko’ina ba ta barin sunan Minjibir a sunanta haka ake kiran sunanta da ƙaramar hukumar daga baya kuma ta ga mutane da yawa sun biyo bayanta su ma suna amsa sunan Minjibir.
Hajiya Zainab Muhammad Sule Minjibir, wacce babbar ma’aikaciya ce da ta yi ritaya a matsayin daraktan manyan makarantu ta jihar Kano, wanda kafin nan ta yi aiki a Kwalejin Ilimi na Sa’adatu a matsayin shugabar sashen tattalin arziƙi ta ce gudunmuwar ga ci gaban ƙaramar hukumar ta ba yau ta fara ba, kuma za ta kuma ci gaba da yi iyakacin tsawon rayuwarta da yardar Allah.
Hajiya Zainab Muhammad Sule ta ce wannan karramawar da aka yi musu don yaba gudunmuwa da suke bayarwa zai yi tasiri wajen ƙara musu ƙaimi sannan ga waɗanada ba a ba su ba, zai saka musu tunani na su ma su yi koyi da ƙwazo su dage domin tallafawa ci gaban al’umma.