
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Muƙaddashin Kwamishina mai kula da tsare-tsare na hukumar FCCPC na ƙasa, Dakta Adamu Abdullahi Sa’in Jama’are ya bayyana cewa duk da hukumar ba ta ƙayyade farashi ba ne, amma sun lura akwai wasu abubuwa da ake a kasuwanni waɗanda suka ga ya kamata su zo ka kunnen ‘yan kasuwa domin a daina yin su saboda sun saɓa wa doka.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙarin bayani ga manema labarai a kan maƙasudin shirya taron yini guda da aka yi a Kano domin faɗakar da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanni a matsayin doka a kan ƙara farashin kayayyaki.
Ya ce akwai ƙungiyoyi da ake da su a kasuwanni daban-daban na masu sayar da nau’i kayn abinci da kayan masarufi ba da sauran kayayyakin sai su zauna a ƙungiya a tsakaninsu su canza farashi su ce yau kuɗin mudun gero ko shinkafa da sauran abubuwa kaza ne. “Wannan ba daidai ba ne,” in ji shi.
Ya yi nuni da cewa kasuwa dole ta zama a buɗe, kowa ya shigo ya faɗi farashin kayansa da ya ga ya dace ya sayar yadda ya gamsu. “To sai suka kawo wani tsari a ce ‘wane kai za ka kawo kaya kaza yau kasuwa, gobe kuma wane ne zai kawo’. Wannan dabara suke na idan aka samu ƙarancin abu a kasuwa farashi zai tashi,” ya jadadda.
Ya ce, “Irin waɗannan ƙungiyoyi sun san in aka ce kowa ya kawo kaya isassu, to kaya zai yi sauƙi, amma ba sa son haka. Hukumarmu ta yi bincike ta gano cewa akwai matsaloli da yawa tun daga gona ma, kafin a kawo kaya kasuwa a sayar. Akwai matsalolin hanyoyi sun lalace, ga jami’an tsaro a hanya suna tare hanya suna karɓar kuɗi da abubuwa makamantan haka,” ya ce.
Sa’an Jama’are ya ce duk da yawancin abubuwan ba hurumin hukumarsu ba ne, amma akwai hukumomi da yake aikin su ne da kwamitoci da suka fi ƙarfin nasu da suke kula da harkar farashi. Don haka abubuwan da suka fi ƙarfinsu sai su ma su miƙa musu, wanda kuma za su iya sai su yi abin da za su yi a kai.
Ya ce misali da aka bayar cewa idan mutum ya ɗauki mota za a kai masa kaya Legas sai ya ajiye N300,000 a gefe yana bai wa jami’an tsaro, wannan dole ne ya fito a cikin farashin kaya.
Ya ce, “Idan ka ɗauki tumatur a mota saboda rashin kyan hanya mota ta lalace ya ruɓe, kana tsammani nan gaba idan ya ɗauka ya ci sa’a ya kai inda za a kai wa zai biya asarar da aka yi a baya? Dole ne sai masayan kaya. Waɗannan abubuwa dole a duba su a yi wani abu a kai. Shi ne muke zuwa mu saurari ‘yan kasuwa mu gaya musu cewa waɗannan dokoki ne a daina karya su.”
Ya ce yanzu faɗakarwa suke nan gaba in an karya dokokin akwai doka a kai, amma wanda ya fi ƙarfinsu sai su miƙa wa wasu hukumomin da ya kamata su yi abin da ya kamata domin farashi ya yi sauƙi.