Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban kwamitin kare haƙiƙin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa, Alhaji Umar Alhaji Bala ya ce nan gaba kaɗan Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi zai sa hannu su ƙone gurɓatttaun kayyaki da suke kamawa.
Ya yi nuni da cewa akwai tarin gurɓatattun kayayyaki da dama iri daban-daban da suka kama waɗanda za su iya cutar da lafiyar al’umma idan suka yi ta’ammali da su, kama daga na masarufi da sauran abubuwa.
Ya ce kwamitin a ƙarƙashinsa a koyaushe suna aiki tuƙuru domin ganin ba a kawo gurɓatattaun kayan masarufi da sauran kayayyaki da za su cutar da al’umma ba.
Shugaban kwamitin kare haƙƙin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa, Alhaji Umar Alhaji Bala ya yi kira ga ‘yan kasuwa a kan su riƙa sassauta farashin kayansu duba da raguwa da ake samu tsadar kaya su tausayawa al’umma.
Ya ce musamman ma yanzu da watan Azumin Ramadan ke kusatowa, hakan zai sa su rabauta da jinƙan Ubangiji a cikin watan Azumi idan suka saukaka kayansu.
Alhaji Umar Alhaji Bala ya jinjina wa jagoransu, Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi bisa irin goyon baya da yake ba su wajen gudanar da ayyukansu cikin nasara.