Tue. Apr 1st, 2025

Yaushe Tashoshin Samar Da Wutar Lantarki Za Su Daina Lalalacewa A Nijeriya?

By Saleh Aliyu Mar 30, 2024

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa ya bayyana cewa an gyara tashoshin wutar lantarki da suka daina aiki a Nijeriya.

Kamfanin ya ce tun da misalin karfe 10 na dare ranar Alhamis aka gyara komai suka koma aiki gadan-gadan.

Manajan hulda da jama’a na kamfanin, Ndidi Mba, ta ce rashin isasshen iskar gas ne ya sa aka samu wannan matsala a ranar Alhamis.

Nijeriya ta fada cikin duhu a ranar Alhamis da yamma bayan daina aiki da babbar tashar samar da wutar lantarki da ke Osogbo na jihar Osun ta yi.

Wata majiya a daya daga cikin kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCo) ta ce kusan duka inda ake samun wutar lantarki a kasar nan ba su da wuta kwata-kwata da hakan ya shafi duka jihohin kasar nan ne 36 kaf.

Daukewar wutar lantarki ya zama ga ‘yan Nijeriya saboda yadda ake samun lalacewa tashoshin samar da wutar lokaci bayan lokaci.

Tambayar da jama’a ke yi ita ce, yaushe za a kawo ƙarshen matsalar lalacewar tashoshin samar da wutar lantarki a kasar nan?

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *