Mon. Mar 31st, 2025

‘Yan Ta’adda Sun Lalata Turakun Wutar Lantarki A Borno Da Yobe

By Jaridar Amana Dec 25, 2023 #Labarai

 

‘Yan ta’adda sun jefa masu amfani da wutar lantarki a jihohin Yobe da Borno cikin duhu bayan sun jefa bama-bamai sun lalata turakun wutar lantarki a jihohin.

Kamar yadda Babban Manajan jami’in Hukumar rarraba wutar lantarki ta Nijeriya (TCN), Ndidi Mbah, ya sanar ranar Juma’a a Abuja, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 21:18 na ranar Alhamis.
Kamfanin ya kara da cewa, ya tura daya daga cikin ‘yan kwangilarsa zuwa wurin da lamarin ya faru da nufin fara aikin sake gyara tasoshin wutar da suka lalace.
Sanarwar ta ce; “Kamfanin samar da wutar lantarki ta Najeriya ya bayyana cewa an lalata daya daga cikin hasumiyansa (tower T372) da ke kusa da kauyen Katsaita a jihar Yobe, inda aka rushe na’urar watsa wutar lantarki mai karfin 330kV, wadda ta ruguza hasumiyar T373 a daidai wannan hanyar.
“Lamarin da ya faru ne da misalin karfe 21:18, 21 ga watan Disamba, 2023, ya haifar da katsewar wutar lantarki a sassan Arewa maso Gabas, wato jihohin Yobe da Borno.
“A yayin da suke sintiri don gano musabbabin yanke wutar lantarkin, injiniyoyin kamfanin TCN sun gano fadowar hasumiya, kuma mutanen kauyen sun tabbatar da cewa sun ji karar fashewar wani abu kafin hasumiyar ta fado,” in ji sanarwar.
“A ci gaba da bincike, injiniyoyin sun gano bama-baman da ‘yan ta’adda suka yi amfani da su wajen rushe hasumiya.
TCN ta yi kakkausar suka kan lamarin, tare da yin nadama da nuna rashin jin dadi ga gwamnati da al’ummar jihohin Yobe da Borno da al’amarsu dangane da halin da za su shiga a kan wannan ta’asa da ‘yan ta’adda suka yi.
Kamfanin ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajen sake gina hasumiya don dawo da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa, kamar yadda jaridar leadership ta ruwaito.
A baya ma dai ‘yan ta’addar sun lalata tashoshin wutar lantarki a wadannan jihohin.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *