
Daga Hadi Bawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa na ci gaba da bin diddigin wani mutum da ake zargi da aikata tsafi bayan wani mummunan kisa da aka yi wa wata budurwa a cikin wani otel da ke karamar hukumar Yola ta Arewa a ranar 18 ga watan Janairu.
An dai yi zargin cewa wani mutum ne da suka shigo otal din tare ya kashe shi tare da yanke masa kai kuma ya arce.
Wanda ake zargin ya bayyana wa masu una da otal don cewa zai je ya yi siyayya, daga nan bai sake dawo ba. Bayan binciken dakin wanda ake zargin, ma’aikatan otal din sun gano gawar budurwar mara kai.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, cikin gaggawa ya ba da umarnin a gudanar da bincike domin kamo wanda ya aikata wannan aika-aika da duk wani mai hannu a cikin wannan danyen aikin domin gurfanar da shi gaban Kuliya.
Rundunar ‘yan sandan ta jaddada muhimmancin hada kai da sauran jami’an tsaro don kare rayukan ‘yan kasa da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu da dukiyarsu.
Kazalika rundunar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, tare da ba su tabbacin cewa dukkanin hukumomin tsaro suna aiki tare domin kamowa da gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifin a gaban kotu.