
Akalla mutane 31 ne rundunar ‘yan sanda ta yi ram da su a yayin da take gudanar da ta kai samame wata maboyar ‘yan ta’adda a Jiihar Gombe.
Jaridar Punch ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mahid Abubakar, yana bayyana haka ga manema Labarai jiya Alhamis a hedkwatar ‘yan sandan jihar Gombe.
Ya ce sun samu wannan nasarar ne ta hannun tawagarta ta ‘yan sintiri ta 999 da suka a wuraren da ake zargin maboyar ‘yan ta’adda ce.
Ya yi bayanin cewa, rundunar da ake yi wa lakabi da Crackdown on Black Spots ta kai ga kama wasu da kayayyakin da ake zargin miyagun kwayoyi ne.
A cewarsa, “A kokarin da suke yi na tabbatar da tsaron jama’a da kuma yaki da munanan ayyuka, da misalin karfe 10:00 na dare, rundunar a karkashin jagorancin jami’ai masu ƙwazo, ta kama wasu mutane tara da ake zargin suna da hannu a ayyukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi. Daga cikin abubuwan da aka kwace a hannunsu akwai busassun ganyen da aka yi imanin cewa tabar wiwi ce da kuma wasu kayayyakin masu da maye.
Abubakar ya lissafa wadanda ake zargin sun hada da Muhammad Mamuda Abubakar mai shekaru 19; Abba Sani, mai shekaru 22; Ismail Usman, mai shekaru 19; Abba Dama Sadiq, mai shekaru 19; Isah Muhammad mai shekaru 25; Aminu Ibrahim mai shekaru 25; Sani Ali, mai shekaru 21; Babayo Lawan, mai shekaru 20 da Usman Muhammad mai shekaru 40.
Da yake karin haske, ya bukaci jama’a da su kasance masu taka-tsantsan, tare da bayar da hadin kai da tsegunta wa jami’an tsaro, domin hadin kai na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.
Ya kara da cewa a wani samame da suka kai na daban makamancin wannan, sun kama sama da mutane 22 da ake zargi da hannu a fataucin miyagun kwayoyi.
“Wannan gagarumin aikin yana nuna jajircewar rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe a kokarin da suke yi na kawar da miyagu daga cikin al’umma.
“Irin wannan aiki yana da muhimmanci wajen tabbatar da doka da oda,” Abubakar ya jaddada.