
Daga Hadi Bawa
A cikin daren jiya Asabar ne, ‘yan bindiga dauke da makamai suka auka wa al’ummar Danhonu da ke Millennium City a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu ‘yan jarida biyu da ke aiki a jaridun The Nation da Blueprint.
‘Yan jaridan Alhaji AbdulGafar Alabelewe da AbdulRaheem Aodu, an yi garkuwa da sune tare da iyanasu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Alhaji Alabelewe shi ne shugaban kungiyar Wakilan kafafen watsa labarai a majalisar jihar Kaduna.
Ganau ya shaida wa majiyarmu cewa, ‘yan bindigar sun auka wa al’ummar ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar, inda suka fara harbe-harbe kafin su yi garkuwa da su.
Ya ce sun yi garkuwa da Alhaji Alabelewe da ’ya’yansa biyu, yayin da suka yi garkuwa da Alhaji Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya.
“Da farko sun dauki Alhaji Abdulgafar da matarsa da ’ya’yansa uku da wata yarinya da suke zauna tare da su kafin su nemi yarinyar ta dawo da daya daga cikin yaran, suka tafi tare da Abdulgafar da matarsa da ‘ya’yansa biyu.
“Sun farfasa musu kofofinsu da tagoginsu tare da cire da shiga gidan bayan sun zare shingen,” in ji shi.
Olayemi, wanda dan gidan Mista Aodu ne kuma yana zaune kusa da gidajen wadanda abin ya shafa, ya ci gaba da cewa: “Sun zo ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar, kuma suka fara harbe-harbe kam mai uwa da wabi.
Da farko suka bude kofar Aodu suka dauko shi da matarsa da karfin tuwo suka bar ‘yarsu mara lafiya.
“Shi kuwa Abdulgafar ta katanga suka shiga gidansa. Kai tsaye suka shiga dakin kwanansa suka dauko shi da matarsa da ’ya’yansu biyu suka fice nan take. Bayan sun fito sai suka fara harbin iska,” in ji majiyar tamu.
Tuni kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kaduna (NUJ) ta fitar da sanarwar manema labarai, inda ta bayyana matukar damuwarta a kan garkuwa da mambobin nata.
Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO), ASP Mansir Hassan, hakarmu ba ta cimma ruwa ba.