Thu. Apr 3rd, 2025

Ya Kamata Tsofaffin Ɗalibai Su Tallafa Wa Ilimi -Hafsat Masigawa

By Saleh Aliyu Feb 3, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An yi kira ga tsofaffin ɗalibai a kan su riƙa ba da gudunmuwa domin cigaban makarantu da suka sami ilimi a ciki ta yadda za su kyautata su domin amfanin ‘yan baya su sami ilimi mai inganci da shi ne ƙashin bayan duk wani cigaba na al’umma.

Hajiya Hafsat Hamisu Ali Madigawa, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗalibai na makarantar Fuƙara’u da Assahaba ce ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da ‘yan jarida.

Ta ce taron tsofaffin ɗalibai abin farin ciki ne ga duk wanda ya saka ƙafauwansa a makarantar su mai albarka, musamman tun da suka gama daga 1982, zuwa yanzu ba a taɓa taro makamancin wannan ba. Suna farin ciki mara misaltawa da gode wa Allah.

Ta ƙara da cewa a matsayinta ta tsohuwar ɗaliba tana cike da kuɗiri a ranta koyaushe na tallafa wa ilimi saboda ko yaya kana so ka ga wurin da ya amfanar da kai ka sami ilimi da ya zamar da kai yadda kake a yau kai ma kana so ka ga wani cigaba a tare da shi. “Don haka ba sau ɗaya ba, ba biyu ba, mun tattauna a kan neman mafita da yadda za mu taimakawa cigaban makaranta,” in ji ta.

Ta yi nuni da cewa, “Ƙofarmu a buɗe take a duk lokacin da buƙata irin haka ta taso, muna buƙatar a riƙa tuntuɓar mu in Allah ya yarda za mu kawo tallafinmu ga cigaban makarantar domin samun cigaba. Maganar tallafawa ba sai kana da shi ba, in dai kana da hamasa na son ka ga ka yi abu komai ƙanƙantarsa, ko yaya yake sai ka ga Allah ya yi maka a cikin kuɗirarsa da buwayarsa. Don haka ‘yan’uwanta tsaffin ɗalibai maza da mata a duk inda suke su dage su haɗa kai su taimaka don kawo wa makarantun cigaba su yi fice yadda za su yi gogayya da dukkanin sauran makarantu”.

Hajiya Hafsat ta ce za su yi duk mai yiwuwa su tura a duk inda suke son saƙon ya je in Allah ya yarda, za su yi wannan ƙoƙarin, kuma su kawo cigaba a gwamnatance da ta ɓangaren harkar kasuwanci da kuma ƙarƙashin ƙungiyarsu ta tsofaffin ɗalibai domin su sami nasarar kai makarantun matakin da ake buƙata.

Sannan ta jaddada kiran ta ga sauran al’umma su farka, “Idan aka yi duba da yadda al’amura ke tafiya na matsalolin ilimi, jihohin muna na Arewa na buƙatar tallafi saboda akwai gazawa a wasu ɓangarorin da ya kamata a ce an haɗa kai domin a gudu tare a tsira tare,” in ji shi.

Hajiya Hafsat Hamisu Ali Madigawa ta ce, “Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf kullum ba da tallafi take a kan abin da ya shafi cigaban ilimi koyaushe su burinsa su ga ilimin nan yadda ake tunanin kudancin ƙasar nan sun yi zarra su tarar da su su ma wuce su wannan kuwa koyi ne da suke da jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da ya ɗora su a kan kishin bunƙasa cigaban ilimi domin jihar Kano ta yi fice.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *