Tue. Apr 1st, 2025

Ya Kamata Mu Ɗinke Ɓarakarmu A PDP A Kano Domin Cimma Nasara -Bagobiri

By Saleh Aliyu Dec 9, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

An jaddada kira ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP musamman jagorori da masu faɗa a ji su yi haƙuri su taho a haɗa hannu waje ɗaya don a gina cigaban jam’iyyar a jihar Kano.

Shugaban Kwamitin Dattawan jam’iyyar na jihar Kano, Alhaji Yahaya Bagobiri ne ya jaddada hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce Kano wuri ne da yake da muhimmanci sosai a siyasa. “Kano jiha ce da take da faɗi, yawan jama’a da tasirin da bai kamata a ce ana samun rarraba a jam’iyyar da ake ganin ita ce mafita ga al’umma daga halin ƙunci da jam’iyya mai mulki ta jefa su a ciki ba,” in ji shi.

Ya ce a matsayinsa na shugaban Dattawan jam’iyyar ba zai fasa irin waɗannan kiraye -kiraye ba har sai ya ga ɓarakar da ke cikin jam’iyyar a cikin gida an ɗinke ta. “Sannan mu fito waje mu kaɗa baza mu yi rawa,” ya jaddada.

Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce suna so a ɗauki darasi daga halin da jam’iyyar ta faɗa a baya, idan ba a ɗauka ba, sai a ga abin da ake so a cimma na gina jihar Kano da tarayyar Nijeriya matsalolin da ake fama da su na yau da kullum, a ce an samu an ɗinke ɓarakar da ake samu, domin su doshi jam’iyyun adawa. “Idan hakan ba ta samu ba, kullum mu da ke jagorori a jam’iyyar zai zama mabiya za su ga kamar akwai hannunmu a wahalar da al’umma ke sha,” ya bayyana.

Ya ce, “Idan muka haɗa kanmu, juya kowace irin gwamnati ba wahala ba ne da yardar Allah, musamman a wannan yanayi na rashin gamsuwa da mulkin da ake musu a ƙasar nan da ya jefa al’umma a mawuyacin halin rayuwa.”

Shugaban Kwamitin na Dattawan na jam’iyyar PDP na jihar Kano, Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce ya yi ƙoƙari ya haɗa kan jagorori guda biyu ya yi magana da su har ma sun zauna sun tattauna kafin ayi zaben jam’iyyar na mazabu sun yi maganganu da su cewa su yiwa Allah su yi hakuri a taho a hadu a hada kai a kafa shugabancin mazabu 484 da kananan hukumomi 44 da jaha kuma har an kai ga za a cimma nasara sai masu hana ruwa gudu suka shiga tsakani ba a sami nasara ba.

“Lokacin ya yi da jam’yiyar PDP za ta sa jadawalinta na gudanar da zaɓe, kuma ba za ta ɗaga ba, shi ne aka ci gaba da yin zaɓuka kowa ya sai fam, kowa ya shiga zaɓe, a tabbatar da nasara ga wanda ya ci zaɓe da shaidar jami’an zaɓe daga uwar jam’iyya,” in ji shi.

Ya ce tunda duk ‘yan jam’iyyar PDP ne dukkansu da wanda ya ci zaɓe da wanda bai ci ba, su taho a haɗu a ajiye bambanci a haɗu a ci gaba da harkokin jam’iyya, haka shi ne abin da ya kamata, domin a zo a fitar da al’ummar Kano daga matsaloli da suke ciki.

Ya ce akwai wasu da aka ce sun tafi kotu a kan yadda aka gudanar da zaɓe bai musu daɗi ba domin sun kashe kuɗaɗe sun sai fam suna ganin za su lashe zaɓuka, hakan bai samu ba, amma yana ganin duk da shi ba Mai Shari’a ba ne, idan ka tafi kotu ka kai waɗanda suka shirya zaɓe ƙara ka ce zaɓe bai yiwu ba, ko ba a yi a kan ƙa’ida ba, a rushe a sake.

Ya ce, “Kotu dai ba za ta ɗauki zaɓe ta bai wa mai ƙara ba, dole jam’iyya za ta miƙawa ta ce a sake gudanar da zaɓe. Ƙila abin da zai faru sai ka ga ya faru sama da yadda aka gudanar dai a baya ma, domin dai jam’iyyar ce dai za ta gudanar da zaɓen ba wani sakamako da za ka iya samu. Abin da ya faru shi zai sake faruwa. Maimakon wannan mai zai hana mu zauna mu haɗa kawunanmu,” cewar Bagobiri.

Ya yi fata shugabanni za su ci gaba da tuntuɓar ‘yan jam’iyya. Duk wanda yake gani an ɓata masa a ba shi haƙuri, wanda yake gani an masa ba daidai ba a ba shi haƙuri a jawo sauran al’umma a ci gaba da tafiya domin a kai ga nasara da yardar Allah,” ya ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *