Wed. Apr 2nd, 2025

Wasan Nijeriya Da Afirka Ta Kudu Ya Ci Rayuka 5

By Saleh Aliyu Feb 9, 2024

Yanzu yanzu an tabbatar da rasuwar mutane biyar kwanaki biyu bayan wasan da aka buga tsakanin Nijeriya da Afrika ta Kudu ranar Larabar da ta gabata a Gasar con Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

Rasuwar wadannan mutane biyar ya biyo bayan fargabar fitar da tawagar kwallon kafa ta Super Eagles da wasu suka yi tsammanin tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu wato Bafana-Bafana za ta yi.

Bayan fafatawar da aka yi a tsakanin kunyoyin kwallon kafa na kasashen biyu a matakin wasan kusa da na ƙarshe da aka yi ranar Larabar.

Bayan ciye lokacin farko da kuma kara lokaci, wasan ya kai sai da aka buga bugun daga Kai sai Mai tsaron gida, inda a ƙarshe Nijeriya ta doke Afrika ta Kudu da ci 4-2.

Ayayin da ake tsaka da buga wasan da ya ɗauki hankalin ɗimbin jama’a, wasu kuwa shi ne ya zama silar ajalinsu a dalilin faɗuwar gaba.

Rahotannin sun tabbatar da cewa Mikail Osundiji mai shekaru 43 ya rasu yana kallon wasan a wani gidan kallo da ke yankin Olomoore na birnin Abeokuta da ke Jihar Ogun.

Ana dai zargin bugawar zuciya ce ta yi ajalinsa a daidai lokacin da alƙalin wasan ya soke kwallon da Nijeriya ta ci ta biyu da dan wasan gaba, Victor Osimhen ya jefa. Sannan ya bai wa Afirka ta Kudu bugun daga kai sai gola a yayin da sakamakon wasan yake 1-0.

Iyalan Osundiji sun tabbatar da cewa lafiya ƙalau ya fita kallon wasan, amma a daidai lokacin da murnar tawagar Super Eagles ke komawa ciki, sai kuwa ya sunkuyar da kansa ya faɗi kasa ba rai. An garzaya da shi asibiti mafi kusa, kafin ya ce ga garinku nan a can.

Haka nan su ma iyalan tsohon Babban Darektan Hukumar Raya Neja Delta, Dokta Cairo Ojougboh, sun ce shi ma faɗuwar gaba ce ta zamo silar ajalinsa.

Hakan ne ƙunshe cikin wata sanarwa ba da tabbaci da Gwamnan Delta, Sheriff Oborewori ya fitar ta hannun Babban Sakataren Labarai na Fadarsa, Mista Festus Ahon a ranar Alhamis.

Ahon ya ce Gwamna Oborewori ya jajanta wa iyalan marigayin da Masarautar Agbor da kuma jam’iyyar APC dangane da rasuwar fitaccen dan siyasar.

Shi kuwa mataimakin babban jami’in kula da harkokin kuɗi na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Alhaji Ayuba Olaitan Abdullahi, ya ce ga garinku nan a dalilin kallon wasan da ake hasashen ya fi kowanne zafi da ɗaukar hankali a duk cikin wasannin da aka fafata a gasar ta AFCON.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Alhaji Ayuba ba tare da ya yi aune ba ya tsinci kansa a cikin yanayi na rashin lafiya yana tsaka da kallon wasan a wani gidan kallo da ke yankin Sango a birnin Ilorin na Jihar Kwara.

Wata majiya ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce Alhaji Ayuba ya kalli wasan har zuwa lokacin da ake shirin soma bugun fanareti, inda ya ce: “Zai tafi gida ya kwanta saboda jiri ya fara ɗaukarsa ba tare da sanin cewa ashe jininsa ne ya zo ba.

“Yana zuwa gida kuwa sai ya zube a kasa, inda aka yi gaggawar miƙa shi wani asibiti a Sango, amma aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, sai dai kafin a duba shi ma ya riga ya cika,” a cewar majiyar.

Jami’ar hulɗa da al’umma ta Jami’ar, Dokta Saedat Aliyu ta tabbatar da mutuwar Alhaji Ayuba cikin wata sanarwa da fitar tana mai roƙon Allah Ya jikansa Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Shi ma dai wani matashi mai yi wa kasa hidima a garin Numan da ke Jihar Adamawa, irin haka ce ta kasance da shi yayin kallon wasan na ranar 7 ga watan Fabarairu.

Majiyarmu ta ruwaito cewa matashin mai suna Samuel ya yanke jiki ya faɗi ne jim kaɗan gabanin soma bugun fanareti.

Samuel, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, an yi gaggawar miƙa shi wani Babban Asibiti, amma kafin wani lokaci kaɗan mai yankan ƙauna ta yi masa halin da ta saba.

Shugaban Hukumar Hidimar Kasa na Jihar Adamawa, Mista Jingi Dennis, ya tabbatar da mutuwar Samuel wadda ya ce ta ɗimauta su.

Ya ce kamar yadda wasu abokan kallon kwallo suka ba da shaida, Samuel ya sanar musu da cewa ba ya son yana kallon kwallo ta kai ga bugun fanareti.

Sun ce ana tsakar kallon ne kuwa sai ya sunkuyar da kansa daga bisani kuma ya zube a kasa wanwar

A birnin Bouake na kasar Ivory Coast da ke karɓar bakuncin gasar ta AFCON, an samu wani hamshakin dan kasuwa dan Nijeriya mai suna Osundu Nwoye, wanda shi ma ya yanke jikin ya faɗi yana tsakar kallon wasa.

Cikin wani saƙo da wani mai suna Chukwudi Iwuchukwu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce attajirin dan asalin Jihar Anambra masoyin kwallon kafa ne na haƙiƙa kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Tambayar da jama’a ke yi ita ce, wannan yanayin da wasu ke samun kansu a ciki a lokacin kallon kafa, tsabar kishin ƙasa ne jawo shi, ko kuwa son ƙwallon ƙafa ne, ko kuma rashin lafiya ce?

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *