Tue. Apr 1st, 2025

Wajibi Ne Ma’aurata Su Zama Masu Biyayya, Haƙuri Da Girmama Juna -Hon. Muhammad Bello Butu-Butu

By Saleh Aliyu Dec 2, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Ɗan majalisa mai wakilar ƙananan hukumomin Rimi Gado da Tofa, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Muhsmmad Bello Butu-Butu, ya yi kira ga ma’aurata ango da amarya su zama masu biyayya da girmama juna, “Domin shi aure ibada ne sunnar Annabi. Mata su bi mazajensu sau da ƙafa a kan kowane umurni da bai saɓa wa shari’a ba,” ya nusar da su.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi jim kaɗan da kammala ɗaurin auren ‘ya’yansa da aka yi a masallacin Rijiyar Zaki a makon jiya, ya ce da babba da yaro da jami’an gwamnati da wakilan Gwamnan Kano da mataimakinsa da ‘yan majalisu na jihar Kano da waɗanda suka zo daga wajenta da wanda suka yi fatan alkhairi daga nesa ya ji daɗi, ya yi farin ciki da yi wa Allah godiya bisa wannan karamci da aka nuna masa.

Hon. Muhammad Bello Butu-Butu ya ce, a matsayinsu na ‘yan siyasa kullum tarbiyya da suke yi wa ‘yan siyasa irin wadda suka gada ce, ta yin biyayya da huƙuri, gaskiya da riƙon amana da yin aiki tuƙuru a duk matsayin da mutum ya sami kansa.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin na jihar Kano ya gode wa al’ummar mazaɓar da yake wakilta na Rimin Gado da Tofa a majalisar Kano bisa irin goyon baya da suke ba shi a kowane lokaci. “A ci gada da ta ya mu da addu’ar ydda za mu cigaba da jajircewa wajen sauke nauyin wakilci da kuka ɗora mana,” ya jaddada.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *