Tue. Apr 1st, 2025

Wajibi Ne A Hukunta Jami’an Tsaron Da Suka Auka Mana A Kaduna Da Zariya -‘Yan Shi’a

By Saleh Aliyu Apr 10, 2024

A taron tunawa da ranar Qudus ta duniya da aka gudanar ranar 5 ga Afrilu, 2024, zanga-zangar lumana a fadin Kaduna da Zariya ta rikide zuwa ban tausayi yayin da dakarun gwamnati suka kai wa masu zanga-zangar da ba su dauke da makamai, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai tare da jikkata wasu da dama.

A yayin wani taron manema labarai da shugaban kungiyar Resource Forum Islamic Movement, Farfesa Abdullahi Danladi ya gudanar jiya Talata a Kaduna, ya ce: “Ranar Qudus ta duniya, ranar hadin kai da Falasdinawa da wadanda ake zalunta a duniya, ana gudanar da taruka da muzahara da ake gudanarwa a duniya. Nijeriya, an kwashe kusan shekaru 40 ana gudanar da taron, amma duk da haka yana fuskantar adawa daga dakarun gwamnati, musamman a yankunan Kaduna da Zariya.

“Muzaharar ta bana, wadda ta samu halartar maza da mata da yara da kuma nakasassu, da nufin nuna goyon baya ga Falasdinawan da kuma yin Allah-wadai da ayyukan da Isra’ila ke yi a Gaza, amma zanga-zangar lumana ta ci karo da karfin tuwo daga jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga gamuwa da mummunan rashi na rayukan marasa laifi.

“Daga cikin wadanda aka kashe akwai Mahmud Umar, Ibrahim Rabi’u, Haidar Ishaq, Mustapha Buruku, Ahmad Mustapha, Mustapha Adam, da Ammar Abdullahi Jihadee, mutuwarsu ta nuna irin ta’asar da masu amfani da hakkinsu na gudanar da taro cikin lumana suke fuskanta.

“A Zariya, inda muzaharar Kudus ta kasu kashi biyu, dakarun gwamnati sun auka wa muzaharar a Sabon Gari, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, wasu da dama kuma suka samu raunuka masu tsananin,” in ji Farfesa Abdullahi Danladi.

Ya kara sa cewa; “Yin amfani da muggan makamai a kan fararen hular da ba su dauke da makami, na nuni da yanayin rashin mutunta muhimman hakkokin bil’adama da ka’idojin dimokuradiyya, maimakon kare ‘yancin ‘yan kasa na gudanar da taro cikin lumana da fadin albarkacin bakinsu, amma sai ‘yan sandan Nijeriya suka mai da martani da tashin hankali da ba su dace ba, wanda ke dagula tunanin adalci, daidaito da dimokradiyya.

“Bayan da gwamnatin Nijeriya ta ba da fifiko wajen kwantar da zanga-zangar lumana, amma ta yi biris wajen magance matsalolin tsaro da suka addabe su, kamar garkuwa da mutane da ‘yan fashi, abin damuwa ne matuka. Jama’a na shakku kan yadda hukumomi ke kokarin tabbatar da tsaro,” ya jaddada.

Malamin Jami’ar ya buƙaci hukumomi su gaggauta daukar matakin kamowa da kuma hukunta wanda ke da hannu a wannan kisan. “Don mayar da martani ga wadannan munanan ayyuka, muna kiran a yi adalci da bin diddigi. Dole ne a gano wadanda suka aikata wadannan laifuffuka tare da hukunta su kan abin da suka aikata.”

Bugu da kari, Farfesa Danladi ya ce, “Al’ummar Musulmi a Nijeriya na tabbatar da ‘yancinsu na gudanar da ayyukan addini ba tare da tsoron fitina ko tashin hankali ba.

“A matsayinmu na ‘yan kasa da musulmi, mun tsaya tsayin daka wajen yin tir da ta’addancin da ake yi wa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, tare da jaddada aniyarmu ta kare hakkin dan’adam da ‘yancin addini,” ya karkare.

Sai dai tun farko ‘yan sandan sun musanta zargin da Yan Shia ke yi masu na aukawa da kashe membonta, inda ta kalubalance su a kan su nuna musu gawarwakin wadanda suka mutu.

Da yake magana a wata hira da kakakin ‘yan sandan, ASP Mansir Hassan ya kalubalanci kungiyar da ta nuna gawarwakin wadanda aka kashe.

“Mun samu labarin cewa mambobin kungiyar IMN da aka haramta za su gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a jihar, kuma nan da nan rundunarmu ta baza jami’anta a wurare masu mahimmanci don hana su tare hanya musamman Ahmadu Bello Way Kaduna.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *