Mon. Mar 31st, 2025

WAHALAR RAYUWA: Ba Abunda Zai Hana mu Zanga-zangar Lumana Domin Nuna Damuwar mu — AYA

By Gazali Haruna Jul 16, 2024 #AYA #Zanga zanga

Kungiyar Arewa Youth Ambassadors ta sake jaddada aniyarta na gudanar da gagarumar zanga-zangar lumana a faɗin Nijeriya musamman babban birnin tarayya, Abuja kan halin Yunwa, wahala, rashin tsaro, da ake fama dashi a Najeriya musamman yankin mu na Arewacin Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Comrade Yahaya M Abdullahi shine ya sake Jaddada hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren yau Litinin biyo bayan zage-zage harma da Sanarwar janyewar zanga-zangar daga wasu tsiraru da suke ta fitarwa tun daga safiyar yau.

“An gayyaci wasu an basu kuɗi, suna ta zagin mu a kafafen yada labarai, wasu ma sun yi kira da a kama ni, wai sun dakatar dani a matsayin shugaban Ƙungiyar, Ni banma san su ba, ban taba ganinsu ba, Ni dai abunda na sani shine fitowa zanga-zangar Lumana babu fashi a Najeriya, musamman babban birnin tarayya, Abuja.

“Duk wanda halin da Najeriya take ciki a yanzu haka to ya fito domin ya nuna damuwar sa, amma idan abunda ake yi a Najeriya yana maka daɗi to kayi zamanka a gida ba komai, amma mu dai zamu fito mu nuna ɓacin ranmu kamar yadda dokar ƙasa da ta Dimokuradiyya ta tanadar.” inji shugaban Ƙungiyar.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *