Wed. Apr 2nd, 2025

Tsohon Kwamishinan Kwankwaso Ya Zama Sabon Shugaban PDP

By Saleh Aliyu Oct 13, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon Kwamishinan Noma a zamanin mulkin Kwankwaso karo na farko. Hon.Yusuf Ado Kibiya ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP na jihar a sakamakon zaɓe da aka gudanar na shugaban jam’iyyar a filin wasan sabon gari ranar Asabar.

Yusuf Ado Kibiya ya samu goyon bayan mafi yawan ‘ya’yan jam’iyyar ne domin suna ganin yana da cancanta da zai iya kai jam’iyyar ga gaci.

Sabon shugaban ya sami nasara ne a kan abokin takararsa, Hon. Nuhu Nura da sauran ‘yan takarar da rinjaye mai yawa.

An rantsar da Hon. Ado Kibiya don jan ragamar jami’yyar ta PDP a jihar Kano da ta dade tana fama da rikicin cikin gida.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *