Tue. Apr 1st, 2025

Tsohon Ɗan Majalisa Ya Kai Wa Jama’ar Tarauni Ɗaukin Gaggawa

By Saleh Aliyu Feb 12, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Tsohon ɗan majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Tarauni, Hafiz Ibrahim Kawu na cigaba da tallafa wa al’ummar yankin ta fannoni daban-daban duk da cewa ba shi ne ɗan majalisa mai ci ba a halin yanzu, amma bincike ya nuna babu abin da ya sauya daga irin hidima da yake musu.

Ɗan majalisar da ya rasa samun nasarar komawa wakilci a majalisar tarayya a zaɓen 2023 hakan ba ta sa ya dakatar da wasu ayyuka da ya somo ba.

Ya cigaba da aiwatar da su musamman na wasu tituna da aka yi a mazaɓu daban-daban na ƙaramar hukumar da cigaba da tallafawa buƙatun al’umma ta ɓangarori da dama.

Haka a ɓangaren ‘yan jam’iyyar su tun daga kan na ƙasa har sama akai- akai suna samun tallafawa da tagomashin tsohon ɗan majalisar da har suke jin tamkar ba su rasa kujerar wakilci da yake musu ba a yankin, suke ganin ba shi da gami da ɗan majalisar yanzu na jam’iytar hamayya da guguwar zaɓe ta kawo da mutanen yankin ke nadama da da na sanin barin Hafiz Kawu suka kawo shi ba ya taɓuka komai.

Ko a ‘yan kwanakin nan tsohon ɗan majalisar na Tarauni, Hafiz Ibrahim Kawu ya tallafawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar ya ba su babura da maƙudan kuɗaɗe don rage musu raɗaɗin rayuwa har wasu ma ya biya musu kujerun zuwa Umara duk da a baya ma ya yi irin makamancin irin wannan tagomashin da har motoci ya bayar.

A wata ganawa da ya yi da ‘yan jarida, Hon. Hafiz Ibrahim Kawu ya ce duba da ba su da gwamnati a jihar Kano shi ya sa yake ba da gudunmuwa ga ‘yan jam’iyyar domin rage musu raɗaɗin da ake ciki na rayuwa da kuma sanar musu irin ƙoƙarin da gwamnatin su ta tarayya ƙarƙashin Ahmad Bola Tinubu take na kawo sauyi da sauƙi a cikin al’amuran talakawa.

Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar su ta APC a kan a hada kai, domin in aka ce za a tafi a wawware ba za a haifi ɗa mai ido ba, idan aka haɗa kai in Allah ya yarda jam’iyyarsu ta APC za ta sami nasara ba maganarsa ko ta wani ba ne, magana ce ta duk wanda yake ƙauna da kishin jam’iyyar ya zo a haɗa kai.

Ya ce shi yana godiya ga Allah domin jam’iyyar APC ta yi musu komai, ba abin da ba ta yi musu ba, ya zama wajibi su tsaya su kare mutunci da muradun jam’iyyar, ya yi takara ya ci zaɓe kuma ya yi takara ya faɗi ya san daɗin nasara da zafin faɗuwa a zaɓe.

Hafiz Kawu ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar a kan su zo a haɗa kai domin Allah shi ne yake yin komai, kuma ya riga ya rubuta waye zai yi mulki, domin ba ya sabon aiki, don haka zai cigaba da daba gudunmuwa domin samun nasara ga jam’iyyarsu ta APC.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *