Thu. Apr 3rd, 2025

Tsaffin Ɗaliban Rimi City Sun Zaɓi Sabbin Shugabanni

By Saleh Aliyu Dec 8, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na makarantar Rimi City, RICOSA, ta gudanar da zaɓen shugabanninta karo na farko a matakin guraben shugabancin guda 18.

An gudanar da zaɓen ne a ranar Asabar a harabar makarantar da dukkan ‘yan takarar suka yi nasara ba tare da hamayya ba da ma sune ke riƙe da shugabancin ƙungiyar suka yi nasara a zaɓen ba tare da hamayya bayan kaɗa ƙuri’u gare su.

Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen ƙungiyar, Magatakardan Farfesa, Auwalu Musa, wanda ɗaya ne daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar ‘yan aji na 1971, ya yaba wa tsoffin ɗaliban bisa ba da haɗin kai da suka yi aka gudanar da zaɓen cikin nasara.

Ya ce sun yi tsammanin tsofaffin ɗaliban ba za su amsa kira da yawa haka ba, amma saboda an ta yaɗawa da kafafen yaɗa labarai da kuma saboda soyayyarsu ga ci gaban ilimi sai ta jawo hankalin tsofaffin ɗaliban sama da dubu suka zo suka zo suka jefa ƙuri’u cikin yanayi mai kyau da sada zumunci a tsakaninsu.

Ya ce an yi zaɓen ne a matakin muƙamai daban-daban guda 18 da Alhaji Aminu Sharif ya samu nasarar zama zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar ta RICOSA.

Sannan ya kuma buƙaci tsofaffin ɗaliban makarantar su riƙa taimaka wa ci gaban makarantar ta ɓangarori da dama kamar samar da ƙarin malamai, kayan aiki, da ƙarin gine-gine a makarantar.

Musa ya yi kira ga tsoffin ɗaliban da su lura cewa tafiyar su tun daga Firamare aji ɗaya zuwa aji bakwai wani abu ne da ba za a manta da shi ba a rayuwa, “Tafiya ce ta riƙo da juna da ‘yan’uwantaka da taimaka wa juna a tsakani musamman masu ƙaramin ƙarfi a tsakaninsu”, in ji shi.

Ya yaba da rawar da tsofaffin ɗaliban makarantar suke taka wajen kawo ayyuka daban-daban a makarantar kamar gina ƙarin ajujuwa da kujerun zama.

Ya yi nuni da cewa, “Batu na gaskiya ita gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin ilimi ita kaɗai ba saboda yawan al’ummarmu. Don haka abu ne mai muhimmanci tsofaffin ɗalibai da sauran al’umma su riƙa taimaka wa gwamnati wajen cigaba ilimi.”

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *