Mon. Mar 31st, 2025

Tsaffin Ɗaliban Firamaren Ƙofar Nasarawa, Kano Sun Gudanar Da Taro

By Saleh Aliyu Dec 27, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Tsofaffin ɗalibai na makarantar Firamare ta Ƙofar Nassarawa, sun gudanar da taron cika shekaru 65 da kafa makarantar.

Taron ya gudana ne a harabar makarantar da ya sami halartar tsarffin ɗaliban da dama.

Shugaban ƙungiyar tsoffin ɗaliban na riƙo, Sadaukin Gumel, Alhaji Abba Muhammad Adamu, ‘ ya bayyana godiya ga Allah bisa yadda ɗimbin tsaffin ɗaliban suka amsa gayyatar, wasu ma da ba su sami zuwa ba, sun yi kira sun faɗi uzurinsu da kuma fatan alkhari ga taron.

Ya ce, “Taron an yi zumunci tsakanin juna. Wannan farawa ma aka yi, musamman ganin yadda tsofaffin shugabannin makarantar da malamai suka ba mu tarbiyya da ilimi ingantacce da har Allah ya kai mafi yawanmu suna manya matsayi a ƙasar nan,” in ji Sadaukin Gumel.

Ya yi nuni da cewa taron yana da muhimmanci. Ya nuna musu haɗa ƙarfi da ƙarfe don taimaka wa makarantar ta samu cigaba da bunƙasa sosai wajen bayar da ingantaccen ilimi ga yara masu tasowa.

Shugaban ƙungiyar tsaffin ɗaliban, ya yaba da ƙoƙari da gwamnatin jihar Kano take wajen raya ilimi, kuma suna kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya waiwayi makarantar tasu a yi mata gyare-gyare da take da buƙata, musamman kayan horor da ɗalibai sana’o’i. Ya kuma yaba da gudunmuwa da tsoffin ɗalibai ke bayarwa.

Sadaukin Gumel ya ce daga irin taimako da tsofaffin ɗaliban suka yi, wasu sun sa an yi rijiya da gina ban ɗakuna irin wanda ɗalibai ke so.

Shi ma Kwamishinan Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha da Ƙirƙire-Kirƙire na jihar Kano, Hon.Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata, ɗaya daga tsaffin ɗaliban ya bayyana jin daɗinsa ga taron da alfahari da jin daɗin cewa yana daga tsaffin ɗaliban makarantar, ya zo ya ga wasu daga tsaffin malamai da suka koyar da su, akwai Malam Ahmad da ya koya musu Turanci har ya iya karanta shi sosai. Haka ma Malam Lawan ya koya musu Llissafi da ta sa har a Jami’a sai da ya yi fice a kai. Wannan gudunmuwa da suka ba su a rayuwar su sun ji daɗinta, kuma suna ganin amfaninta.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Kwamishinan Yusuf Ibrahim Ƙofar Mata ya ce, taron ya yi kyau, ya ga manyan mutane, domin makaranta ce babba. “A matsayinna na Kwamishina a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha a yanzu za mu ga yadda za mu taimaka sosai wajen cigaban makarantar nan,” inji shi.

Ya ƙara da cewa taron yana tuna musu baya da aka haɗu da waɗanda suka sami cigaba, don haka tsaffin ɗalibai su zama masu tuna baya da yin wakilci nagari a kan abin da ya shafi al’umma, kuma babban amfanin taron shi ne a duba baya a taimakawa juna.

A nata ɓangaren, shugabar makarantar Firamare ta Ƙofar Nasarawa, Nafisa M. Tahir Yakasai da take bayani, wacce ita ma ɗaya ce daga tsofaffin ɗaliban makarantar ta ce, ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba, da yadda aka gudanar da taron, domin nasarar da aka samu ita ce, waɗanda suka daɗe ba su ga junansu ba, sun gamu dama ba a taɓa yin makamancin irin wannan taron ba, sai yanzu.

Ta ƙara da cewa tana alfahari da cewa ita ce ta zo da tunanin a yi taron da aka gudanar kowa ya ji dad ɗi shi ne babban farin cikinta.

“Duk da mun ɗan sami kule wajen haɗo kan ɗaliban, amma a hankali da taimakon Allah da wasu manya daga tsofaffin ɗalibai muka cimma nasara,” in ji shugabar makarantar.

Hajiya Yakasai ta ce, a matsayinta ta shugabar makarantar a halin yanzu zuwan ta makarantar Firamaren Ƙofar Nasarawa sun same ta da ƙarancin ɗalibai da kayan aiki da take da buƙatar abubuwa da yawa, amma irin ƙwazo da ta yi da haɗin kan sauran malamai abubuwa na gyaruwa ana kawo ɗalibai makarantar da ƙoƙarin gyare- gyare da ake yi. “Muna fatan tsofaffin ɗalibai ma za su taimakawa cigaban bunƙasar makarantar,” ta jaddada.

A lokacin taron an karrama wasu daga tsofaffin ɗaliban da shaidar yabo bisa gudunmuwa da suke bayarwa wajen taimakawa cigaban makarantar.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *