Wed. Apr 2nd, 2025

Tinubu Ya Ba Da Umarnin A Bude Rumbuna A Fito Da Kayan Abinci

By Saleh Aliyu Feb 9, 2024

Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta fito da kayan abinci daga cikin rumbunan da ake tanadi don rage wahalhalu a kasar.

‘Yan Nijeriya dai na kokawa kan tsadar rayuwa, inda suke kara matsin lamba ga Gwamnatin Tarayya da ta sauya yanayin.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci za ta saki kimanin tan dubu arba’in da biyu na masara, gero, gari da sauran kayayyaki da ke cikin rumbunan da aka tanada.

Idris, ya shaida wa manema labarai na fadar Aso Rock bayan taron kwamitin shugaban kasa na musamman kan ba da agajin gaggawa a fadar jiya Alhamis, ya ce tuni aka cimma matsaya a kan haka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Idris yana cewa: “Na farko shi ne an umurci Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci da ta saki kimanin ton 42,000 na masara, gero, gari, da sauran kayayyakin masarufi a cikin dabarun da aka tanada domin samar da wadannan kayayyaki ga ‘yan Nijeriya.

“Na biyu kuma shi ne mun yi taro da kungiyar sarrafa shinkafa ta Nijeriya, wadanda ke da alhakin samar da shinkafa, kuma mun bukaci su bude shagunansu.

“Sun gaya mana cewa za su iya bayar da tabbacin samar da ton 60,000 na shinkafa. Za a samar da wannan, kuma mun san cewa hakan ya isa ya dauki ‘yan Nijeriya nan da wata daya zuwa makonni shida, watakila har zuwa wata biyu.

“Yanzu haka kuma gwamnati na duba yiwuwar, idan har ya zama dole a matsayin matakin wucin-gadi, a shigo da wasu daga cikin wadannan kayayyaki nan take daga waje ta yadda za a samar da wadannan kayayyaki ga ‘yan Nijeriya nan da nan cikin makonni biyu masu zuwa.

“Yanzu gaba daya tunanin hakan shi ne a rage farashin wadannan kayayyakin abinci, kuma wadannan matakai ne da za a dauka nan take, wannan lamari ne na gaggawa, kowace al’umma na fuskantar matsalolin gaggawa irin wannan, ba shi ne karon farko da hakan ya faru ba. Kasashe da dama na duniya sun fuskanci hakan.

“Lokaci ya yi da za mu fuskanci wannan kalubalen, gwamnati za ta mayar da martani mai kyau, kuma tuni ta fara mayar da martani yadda ya kamata. Shugaban kasar ya ba da umarnin cewa duk matakan da za ta dauka da za a ba ‘yan Nijeriya abinci a farashi mai sauki a dauka. Wannan shi ne abin da taƙaitaccen wannan taron ya kunsa.

”Kungiyar kwadago ta kasa ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin tarayya kan tabarbarewar tattalin arziki da tsar rayuwa.

Ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba ta gani in gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *