Mon. Mar 31st, 2025

TAWAGAR YAKN NEMAN ZABEN HON LION TA ZIYARCI AKWATINAN MAZABAR DAUDAWA

By Gazali Haruna Jan 27, 2024 #Katsina #Siyasa

Daga Awwal Jibril ‘Yankara


Dan Majalisar taraiya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa
Hon. Jamilu Muhammad Lion ya ziyarci Akwatinan Mazabar Daudawa da ke Karamar Hukumar Faskari Jihar Katsina Domin neman Alfarmar su da su fito su Sake zaben sa a Ranar 3-2-2024 domi cika Umarnin Kotu da ta Bayar na chanza Zabe wasu Akwatina Guda hudu a gundumar Mazabar Daudawa da wasu Guda 16 a Karamar Hukumar Kankara duk a Jihar Katsina


Dubanin Al’ummar Mazabar Daudawa ne sukayi dafifi bakin akwatin su da za a chanza zabe domin tarbar Dan Majalisar wanda Al’ummar wannan yanki sukaima suna Fadi da cikawa.

Dan Majalisar da tawagarsa sun zagaya akwatinan da zaa chanza zabe guda hudu dake Mazabar ta Daudawa a karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina
akwatin sune kamar haka

Daudawa,kwankiro, Kanon Haki Da Tudun malamai duka a Mazabar Daudawa dake karamar hukumar Faskari jihar Katsina

wannan tawagar tasamu Jagorancin na Musamman karkashin Jagorancin Alhaji kabir Maiwada Daudawa da shugaban riko na Jam’iyyar PDP a karamar hukumar Faskari Hon Khalid Adamu Bilbis da sauran masu fada a Jami’ar PDP a karamar hukumar Faskari.

wannan ziyara ta tabbatar da cewa Lion ya cika ma fadi da cikawa domin ko ina mukaje godiya suke da aikin da suka gani kasa ba labari ba.
Inji Mataimaki na Musamman ga Dan Majalisar Adamu Nura Tina da Yake zantawa da wakilin Mu, bayan kammala Ziyarar

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *