Mon. Mar 31st, 2025

Su Wa Suka Kai Wa Ɗan Takarar Ƙaramar Hukumar Hari A Kano?

By Saleh Aliyu Oct 20, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Wasu gungun matasa da ake kyautata zaton ɓarayi ne da ‘yan daba, sun auka wa tawagar ɗan takarar neman shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano da kewaye, Hon. Salim Hashim da jifa da duka da sara da miyagun makamai a wani yanki a unguwar Gandun Albasa a lokacin da suke yin zagayen yaƙin neman zaɓe a ranar Asabar.

Wata majiya ta gani da ido ta tabbatar wa manema labarai cewa, dan takarar da mutanensa suna tafe cikin tsari da natsuwa, ba zato ba tsammani sai wasu gungun matasa suka far musu da jifa, duka da ƙwace hakan ya jawo jikkata mutane dama da yi musu ƙwacen wayoyi da lalata ɗimbin motoci na wasu daga ‘yan tawagar.

Sai dai wasu a yankin da muka zanta da su a kan lamarin sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ba shi da alaƙa da siyasa suna dai ganin wasu gungun ɓata gari ne suka yi amfani da yanayin suka auka wa tawagar motocin ɗan takarar saboda kawai su yi musu sata da ƙwace.

Wata majiya ta tabbatar da cewa inda aka yi abin ko a kwanakin baya ma a lokacin zanga-zangar tsadar kayayyaki a nan yankin ne wasu bata-gari suka shiga wata makarantar Islamiyya ta shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kano suka sace kayan abinci da suka haɗa da buhunan shinkafa da aka ajiye ana ciyar da ‘yan makaranta da marayu.

Wakilinmu ya ga ɗimbin motoci da ‘yan daban suka cire musu wasu muhimman kayayyakin jikinsu suka tafi da su suka kuma lalata sama da guda 14 na ‘yan tawagar rakiyar ɗan takarar.

Ɗan takarar na karamar hukumar Birnin Kano a jam’iyyar NNPP, Hon. Salim Hashim Gwangwazo ya tabbatar mana da faruwar lamarin da cewa suna cikin tafiya aka auka musu da jifa da sara da ƙwace hakan ya jawo asara mai yawa har sai da jami’an tsaro kawo ɗauki.

Jama’a da dama sun nuna takaici da rashin jin daɗinsu ga abin da ya faru da cewa hakan bai dace da tsari na mutuntaka da wayewa ba. Sun yi kira ga jami’an tsaro a kan su zaƙulo waɗanda suka yi abin don yi musu hukunci daidai da tanadin doka.

Mun tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda na jihar Kano domin jin ta bakinsu a kan lamarin har zuwa lokacin rubuta labarin ba su ce komai a kai ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *