Wed. Apr 2nd, 2025

Su Wa Ke Barazana Ga Rayuwar Gwamnan Katsina?

By Saleh Aliyu Feb 9, 2024

Gwamnan Katsina Malam Umar Dikko Radda ya yi zargin cewa ‘yan ta’addan da kuma wasu mutane suna yi wa rayuwarsa barazana saboda kokarin sa na tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Radda, wanda ya bayyana haka a wajen wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaka don lalubo hanyar shawo kan matsalolin tsaro da ke ci wa Jihar tuwo a kwarya da aka yi jiya Juma’a a gidan geamnatin Jihar, ya tabbatar da cewa rahotannin tsaron da yake samu ne suka tsegunta masa barazanar da ake yi wa rayuwarsa.

Duk da yake Gwamna Radda bai ambacin sunan masu yi wa rayuwar tasa barazana ba, amma ya tabbatar da cewa ko kusa babu abin da zai razana shi balle ya kau da kai daga alkawarin da ya yi wa jama’ar jihar Katsina na kakkabe ‘yan ta’adda.

Radda ya bayyana cewar nasarar da ake samu a kan ‘yan ta’addan shi ne ke musu zafi, saboda haka jami’an tsaro za su ci gaba da aikin su wajen ganin an samu cikakken zaman lafiya a jihar.

Kazalika ya yi alkawarin kafa kwamitin da zai aiwatar da yarjejeniyar da taron na masu ruwa da tsakin ya cimma.

Kazalika ya tabo batun karancin abinci da jama’a ke fuskanta, tare da daukar alkawarin daukar matakan da suka dace don yi wa tufkar hanci, kamar yadda gidan radiyon RIF ya ruwaito.

Taron ya samu halartar sarakunan Katsina da Daura; Mai Martaba Abdulmumini Jibrin, da Mai Martaba Umar Faruk Umar da kuma shugabannin hukumomin tsaro da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa.

A kwanakin baya ne Gwamna Radda ya kaddamar da rundunar sa-kai da ake ganin sun fara karya lagon ‘yan bindigar da suka hana zaman lafiya a wasu sassan jihar.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *