Tue. Apr 1st, 2025

‘Son Zuciya Ya Sa Na Kashe Abokina Saboda Naira Miliyan 3’

By Saleh Aliyu May 10, 2024

Wani magidanci a Kano ya bayyana yadda son zuciya da neman son tara abin duniya, ya ja shi ga kashe abokinsa a kan Naira miliyan uku.

Sadik Zubairu mai shekaru 35 da ke zaune a unguwar Hotoron Arewa a karamar hukumar Nassarawa, Kano, ya bayyana yadda ya yaudari abokinsa, Bello Bukar Adamu tsohon ma’aikacin Hukumar Rarraba Wutar Lantarki da ke Kano (KEDCO) mai shekara 45 ya kashe shi.

Kamar yadda ya bayyana wa ‘yan sanda, Zubairu ya tabbatar da cewa Adamu ya ba shi kuɗi Naira miliyan uku ne don ya sama masa aiki a Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya (FIRS), amma sai ya yanke shawarar ya kashe shi don ya mallake Kuɗin da motarsa.

Zubairu, ya bayyana cewa a cikin gidansa suka kashe Adamu shi da wasu mutane biyu, ta hanyar dukansa da tabarya da kuma wani karfe har ya mutu, ya bayyana nadamarsa kan wannan ta’asar da ya aikata, tare da kira ga mutane su wadatu da abin da Allah ya hore masu, bare da hangen na wani ba.

Tun da farko dai an bayyana bacewar Bello Bukar Adamu a ranar 5 ga Mayu, 2024, inda aka gano gawarsa kusa da ƙauyen Bechi Zawaciki daura da Eastern Bypass a karamar hukumar Kumbotso a Kano.

Likitoci a asibitin Aminu Kano sun tabbatar da muruwarsa bayan binciken da suka gudanar.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Hussain Gumel, ya bayar da umarnin a kama waɗanda ake zargi da aikata laifin cikin sa’o’i 24, kuma an kama shi da misalin karfe 23 na safe, sannan kuma an gano motar marigayin kirar Toyota Corolla a ranar 04/05/2024, tare da tafiya da wayarsa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ya bayyana cewa, an zargi Sadik Zubairu, ya kashe amininsa Bukar ne a kan Naira miliyan uku.

Yayin da ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin kan wannan lamari mai cike da bakin ciki, Kwamishinan ‘yan sandan ya kara jaddada aniyar rundunarsa na yakar miyagun laifuka a kowane fanni da kuma ci gaba da yin aiki tukuru wajen kare rayuka da dukiyoyin daukacin mazauna Kano.

Ya tabbatar da cewa da zarar sun kammala binciken za su gurfanar fa da Zubairu a gaban Alkali don ya fuskanci hukunci.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *