Tue. Apr 1st, 2025

Shugaban Kasa Tinubu ya sa hannu a kan kasafin kuɗin 2024

By Gazali Haruna Jan 1, 2024 #Kasafi #Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya sa hannu kan ƙudurin kasafin kuɗin bana na sama da naira tirliyan 28 zuwa doka, jim kaɗan bayan komawarsa Abuja daga Lagos.

Ya dai bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa zai bi diddigi wajen ganin yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin, ya kuma ce ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomi su riƙa bayar da rahoton yadda suke aiwatar da kasafin kuɗin wata-wata ga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar ta ce manyan ɓangarorin da kasafin kuɗin ya mayar da hankali a kansu akwai tsaron ƙasa da samar da tsaro a cikin gida, samar da aikin yi da daidaita harkokin tattalin arziƙi da bunƙasa yanayin zuba jari da rage talauci.

Shugaba Tinubu ya nanata cewa ƙudurinsa na kyautata harkokin zuba jari da ƙoƙarin samar da al’umma mai bin doka wadda ba za ta fifita kowanne mutum ba, zai fara da muhimman sauye-sauye a ɓangaren shari’a, wanda kuma an samar da kuɗaɗen yin su a cikin kasafin kuɗin.

“Samar da kuɗi ga ɓangaren shari’a wani muhimmin ƙuduri ga ƙoƙarinmu wajen tabbatar da wata al’umma mai bin doka da tsayawa a kan daidai. An ƙara kuɗaɗen da ake warewa ɓangaren shari’a daga tushe daga naira biliyan 165 zuwa naira biliyan 342,” cewar shugaban ƙasar.

Sanarwar ta ce muhimman alƙaluma a cikin kasafin kuɗin su ne manyan ayyuka naira tirliyan goma da ayyukan yau da kullum naira tirliyan 8.8 sai biyan basuka tirliyan naira 8.2 sai kason tallafi na doka daga asusun tarayya naira tirliyan 1.7.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *