
Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ya mika sakon gaisuwar Ramadan ga al’ummar Musulmi.
A cikin wani sako da ya raba wa manema labarai yau Litinin, Jalal Ahmad Arabi, ya bayyana cewa, watan Ramadan lokaci ne mai tsarki na ibada, kankan da kai da kuma sadaukarwa, tare da jaddada muhmmancin dagewa da mika wuya wajen fuskantar kalubale.
Ya tabbatar da cewa Alkur’ani Mai Tsarki ya umurci Musulmi da su jure wa fitintinu daban-daban, inda Allah Ya ce: “Kuma lallai ne za mu jarraba ku da wani abu na tsoro da yunwa da nakasar dukiya da rayuka da ‘ya’yan itace, kuma ku yi bushara ga masu hakuri.” (Sura ta 2, Aya ta 155).
“Tabbas kalubale na iya wanzuwa a cikin al’umma, amma wani bangare na imanin Musulmi shi ne sanin cewa hikimar Allah tana cikin kowane fanni na rayuwa, gami da lokutan yunwa da wahala, tare da hakuri da jarabawa, da tausayawa.
“Yayin da muka fara wannan aiki na horon ruhi, mu yi kokari wajen kara karfafa imaninmu da mika wuya ga Allah, mu sami karfi da juriyar fuskantar gwajin da ake yi mana a wannan lokacin. Mu kara zage damtse wajen tallafa wa juna ta hanyar kyautatawa, tausayi da fahimta.
“Ramadan ya zama tunatarwa a kan sadaukarwar da muka yi da juriya da karfafa alaka mai zurfi da Allah da kuma fahimtar hadin kan da ke tsakaninmu,” in ji shi.
A cikin sanarwar, Arabi ya bukaci dukkan Musulmin Nijeriya da su rungumi Azumin watan Ramadan da zuciya daya, tare da sanin cewa kalubale na ba da damammaki na ci gaban ruhi.
Ya yi fatan wannan wata na Ramadan zai ya kawo albarka, zaman lafiya, da sabunta azama ga kowa da kowa.