Tue. Apr 1st, 2025

Shugaban Ƙaramar Hukumar Roni Na Samun Kyakkyawan Yabo Daga Al’umma

By Saleh Aliyu Feb 6, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban ƙaramar hukumar Roni da ke jihar Jigawa, Dakta Abba Ya’u, na samun yabo daga al’ummar yankin bisa irin matakan da yake ɗauka na tallafawa matasan yankin wajen gina su a kan ilimi da kyautata jin daɗin rayuwarsu.

Shugaban, wanda ya yi duba da muhimmancin ilimi, wanda shi ne hasken rayuwa, ya ɗauki nauyin tura ɗalibai ‘yan asalin yankin yin karatu a wasu manyan makarantu a ciki da wajen jihar Jigawa.

A wani jawabi da Dakta Abba Ya’u Roni ya yi ga wasu rukunin ɗalibai da da ya ɗauki nauyi tura su karatu ya yi nuni da cewa, “Duk wanda yake da ilimi za a ga rayuwarsa tana yin kyau. Idan kana son gina al’umma ka bai wa wannan al’umma ilimi. Don haka a matsayinmu na gwamnati a wannan lokaci muke bai wa harkar ilimi muhimmanci, ” in ji shi.

Shugaban ya ja hankalin ɗalibai da aka tura karatu su mai da hankali su jajirce su sami ilimi domin a samu masana a fannoni daban-daban a cikinsu, kama daga likitoci, lauyoyi da sauran fannoni na bunƙasa cigaban rayuwa.

Ba kawai harkar ilimi ba, shugaba ƙaramar hukumar Dakta Abba Ya’u Roni yana ƙoƙarin bai wa iyaye mata da matasa da dattawa tallafi ta yadda za su zama masu dogaro da kai wannan tasa yake samun kyakkyawar shaida da yabo daga al’ummar yankin.

Ko shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Jigawa Hon. Lawan Ɗansure, ya yaba wa Hon. Abba Ya’u Roni da cewa ayyukan da yake da ma suna yi masa kyakkyawan zaton zai yi su, domin daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. “Domin idan ana gadon mulki, ya gada, shi ya sa ba ma mamakin irin ayyuka da yake,” ya tabbatar.

Hon. Lawan Ɗansure ya ce tunda Dakta Abba Ya’u Roni ya zama shugaban ƙaramar hukumar Roni ranakun aiki da wanda ba na aiki ba ma yana zuwa ofis ya zauna ya saurari buƙatun jama’a.

“Mun gode wa Allah da ya zaɓa mana Dakta Abba Ya’u a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Roni ya sauke nauyin shugabanci da aka ɗora masa,” ya jaddada.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *