Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban ƙaramar hukumar Fagge Hon. Salisu Usman Masu ya yi ƙarin albashi na nunkin ba nunkin abin da ake biya a baya ga ma’aikatan wucin-gadi na sassa daban-daban na ƙaramar hukumar.
Ya bayyana cewa maƙasudin ƙarin shi ne zuwan sa ƙaramar hukumar ya sa a ɗauko masa cikakken adadin yawan ma’aikatan wucin-gadi da ake da su, da aka kawo ya ga sun kai sama da 300 ana ba su albashin da bai wuce N2,500, wasu ma ƙasa da haka a wata.
Don haka sai ya kafa kwamiti da za a tantance masa gaskiyar adadin yawan ma’aikatan, ƙarƙashin jagorancin Kansilan Mazaɓar Fagge C. Hon. Sanusi Shariff Kantoma saboda mutum ne mai gaskiya da amana ya umurce su su bi ɗaya bayan ɗaya sassan ma’aikatu su tabbatar da gaskiyar yawan ma’aikatan don kaucewa almundahana.
Ya ce da suka kammala sun kawo masa rahoto na gaskiyar adadin yawan ma’aikatan, ‘yan kwamitin sun yi aiki sosai na tabbatar da gaskiya sun gano mafi yawan mutane da ake biya babu su waɗanda aka tabbatar ma’aikata ne ba su fi 100 da ɗoriya a tsakanin masu kula da maƙabartu, asibitoci da makarantu da sauran sassa.
Sun tabbatar da adadin ma’aikatan na wucin-gadi sai ya ga ba daidai ba ne a ce mutum na aiki, ana ba shi albashin da bai wuce 2,500 a wata ba, don haka ya daidaita musu albashin ya ce duk a riƙa biyan su N10,000. Ƙaramar hukumar ta saki kuɗaɗen da ake biyan su.
Hon. Salisu Usman Masu ya ce kuma sun sa idanu duk wanda aka samu yana yi wa ma’aikatan ɗungushe wajen biyansu haƙoƙinsu za a ɗau mataki mai tsauri a kansa, domin suna kwaikwayo ne da tsarin gaskiya na Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da jagoransu na Kwankwasiyya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, duk wanda suka ba shi amana ya yi abin da bai kamata ba, sai ya yaba wa aya zaƙi.
Ya ce, “Ma’aikatan ƙaramar hukumar sun yi matuƙar murna da wannan ƙarin. Don in ka taimakawa na ƙasa, Allah zai taimake ka. Dama a ce muna da isassun kuɗi ne a da mun ƙara musu fin haka ma. Ma’aikatan su ke ɗawainiya kullum,” in ji shi.
Hon. Masu ya ce zuwan su ƙaramar hukumar Fagge cikin wata biyu da ‘yan kwanaki sun yi tsari na tallafawa mutane, musamman marasa lafiya da masu neman kuɗin biyan haya da waɗanda za su aurar da ‘ya’yansu mata, amma ba su da hali, sun bai wa mutane sama da 300 gudunmuwa kama daga wanda aka ba su ₦500,000, wasu ₦250,000, wasu ₦300,000, ba kuma wanda aka bai wa ƙasa da ₦100,000, kuma za su cigaba da ba da irin waɗannan tallafi iya iyawarsu.
Ya ce akwai ayyuka da suke yi na kai tsaye a ƙaramar hukumar da suka haɗa da na kwalbatoci, sun ɗauki sassan yankunan ƙaramar hukumar uku ƙwaryar Fagge da Arewacin Fagge da Sabon Gari suna kwalbatoci guda biyu a kowace shiyya masu inganci, yanzu an yi guda huɗu ma, saura biyu da za a yi a Sabon Gari a matsayin aikin samfur ne.
Hon. Salisu Masu ya ce shi a tsarin sa, da ya yi aiki guda 100 mara inganci, gara ya yi 10 masu inganci su komai suna amfani ne da kayan aiki masu inganci da za su yi ƙarko. “Irin waɗannan ayyuka za mu cigaba da yin dukkan ayyuka da za mu yi wa al’umma. Yanzu haka akwai makarantu da za mu yi musu gyara a kyautata su a yankin,” ya jadadda.
Hon. Salisu Usman Masu, wanda ya bayyana cewa cikar Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf shekaru 62 a duniya da cewa ko ba komai kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin yau yana ƙasa da shekara biyu kan kujerar mulkin Kano, amma ya kawo ɗimbin cigaba a Kano. “Muna fatan Allah ya ƙara masa basira, ya cigaba da irin ayyuka na alherai da yake bijirowa da su,” ya ƙarkare.