
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II ya naɗa Alhaji Auwalu Mudi Yakasai sakataren kungiyar kwadago na jihar Kano a matsayin Ɗanmalikin Kano.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan naɗin da aka yi masa a ranar Juma’a a fadar Kano, Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya bayyana godiyarsa ga Allah da gode wa Sarkin Muhammad Sanusi bisa wannan naɗin da ya yi masa.
Ya ƙara da cewa a tarihi gidansu ya shafe sama da shekara 130 rabon su da sarautar sai yanzu Allah ya waiwaye su, mai martaba Sarkin Kano ya waiwaye su ya dawo musu da wannan sarautar.
Ya yi nuni da ce wannan abin a yaba ne, a gode wa Sarkin Kano a yi masa addu’a, ba abin da za su ce sai “Allah ya taimaki Sarki, ya kare shi, ya kyautata bayansa, kamar yadda ya waiwayi zuri’arsu, Allah ya waiwayi nasa, ya ƙara wa mahaifiyarsa lafiya, ya jikan mahaifinsa,” in ji Ɗanmalikin Kano.
Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya yi nuni da cewa a cikin mutane, kowa yana da irin ƙaddararsa. “Allah ya ƙaddara ni ne zan ɗauko kitse a wuta na samun wannan sarauta wadda Allah da ya ƙaddara hakan shi ne, kuma ya san me yake nufi ba su da abin da za su yi sai dai su ci gaba da gode masa.”
Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya yi kira ga al’ummar musamman matasa a kan su ji tsoron Allah su sa gaskiya a duk abin da suke yi, sannan su girmama iyaye da shugabanci da shugabanni idan aka riƙe wannan za a zauna lafiya a sami ci gaba da albarka a rayuwa.
Sabon Dan mulkin na Kano Alhaji Auwalu Mudi Yakasai ya ce aikinsa a fadar Sarkin Kano aikin Sarki ne, kuma shi Sarki ba a yi masa shisshigi a ayyukansa.