
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sarkin Yamman Kano Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya bayyana godiya bisa dama da Allah ya ba shi aka zaɓe shi a cikin mutane da yawa ba domin ya fi wani ba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi ya ga ya cancanta ya naɗa shi a sarautar Sarkin Yamma.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a gidansa jim kaɗan bayan naɗin da aka yi masa.
Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya ƙara da godiya ga Allah bisa wannan sabuwar sarauta da aka ba shi wacce ba a taɓa yin ta a Kano ba, ita ce ta farko da Allah ya nufa shi aka soma yi wa a wannan lokaci.
Sabon Sarkin Yamman na masarautar Kano Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya ce kasancewar sarautar baƙuwa ce a Kano suna shirye da yin biyayya da yin ayukka da Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi zai ɗora musu nauyin gudanarwa a masarautar.
Ya ce muhimmin abin da za su yi shi ne su taimaka wajen ba da shawara wajen yadda za a tafi da mulki a ƙasar Kano yanzu abin da za su yi ke nan. “Ina matuƙar farin ciki da ni na soma rabauta da sarautar Sarkin Yamma. Ina godiya ga Allah bisa dama da ya ba ni,” in ji shi.