
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yana cikin waɗanda suka halarci jana’izar fitacciyyar jarumar finafinan Hausa, Saratu Gidaɗo.
Jana’izar, wacce aka gudanar a harabar babban Masallacin Juma’a da ke fadar Sarkin Kano, ta samu halartar dimbin jama’a.
A cikin daren jiya ne Allah ya dauki ran jarumar Kannywood, Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso sakamako gajeruwar rashin lafiya.
Iyalan Daso sun bayyana cewa an yi hira da ita jiya a cikin dare, ita ce ma ta buƙaci a je a kwanta saboda a yi shirin Tahajjud. Sai dai ba a tashi da ita ba.
Saratu Gidaɗo, wacce aka haifa ranar 17 ga Janairun 1968 a Gombe, ta yi fice a masana’antar Kennywood wajen taka duk rawar da aka buƙaci ta yi. Ta fi yin fice iya taka rawar makirci da suddabaru, takan taka kowacce irin rawa domin ta zama tauraruwa.
Bayanan da muka samu sun tabbatar da cewa Saratu Gidaɗo ta fara fitowa a fim ne a shekarar 2000 a wani fim mai suna Linzami Da Wuta, wanda kamfanin Sarauniya Movies ya shirya.
Sauran fina-finan da ta fito sun hada da Nagari, Gidauniya, Mashi, da Sansani.
A daidai lokacin da ake ci gaba da alhin rashinta, jama’a sun tambayar wa zai maye gurbinta a irin rawar da take takawa a Kennywood?