Thu. Apr 3rd, 2025

Sakacin Gwamnati Ne Ya Mai Da Noman Auduga Baya -Sarkin Augudar Kumo

By Saleh Aliyu May 15, 2024

Daga Abubakar Rabilu Gombe

Alhaji Sadiq Ado Matamaimakin shugaban kungiyar manoma da masu kasuwancin auduga na Nijeriya, kuma shugaban na shiyyar Arewa maso Gabas ya ce, sakacin gwamnatoci ne ya mai da harkar noman auduga baya.

Alhaji Sadiq Ado Sarkin Audugar Kumo, wanda ya bayyana hakan a wata hirar da ya yi sa manema labarai, ya ce, amma yanzu da suka juyo, don haka darajar noman zai dawo.

Ya ce idan aka habbaka noma da kasuwancin auduga, hatta masaku da suka durkushe za su farfado, kuma aikin yi zai wadata a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Alhaji Sadiq ya kara da cewa yadda Dalar Amurka take da daraja yanzu da an noma audugar za ta yi farashi sosai wanda noman da ‘yan kasuwa za su ci moriya fiye da yadda ake tunani domin dama safarar auduga na ta’allaka da farashin Dala saboda kasuwanin kasashen waje.

A cewar sa an duba an ga babu abin da ke samar da aikin yi a tsakanin al’umma kamar noman auduga, kama daga kan masu noman ta da sayar da ita da masu gurzarta zuwa kamfanonin saka da suke saka tufafi da sauran su.

Alhaji Sadiq Ado, ya kara da cewa kawar da kai da gwamnati ta yi a harkar noman nudugar shi ne ya jawo koma bayan kasuwancinta, amma yanzu a jihar Gombe gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya mayar da hankali wajen ganin an farfado da ita, inda ya hada kai da wasu Turawan kasashen waje dan bunkasa harkar.

Har ila yau ya ce, a shekarun baya shirin nan na gwamnatin tarayya na Anchor Borrowers ya taimaka wajen kara habbaka harkar noman wanda ba a san yanzu ko wannan gwamnatin za ta ci gaba da shi ba ganin cewa ta yi shiru a kai, amma da za ta ci gaba da harkar noman auduga ya wuce inda ake tsammani.

Ya ce rashin noma audugar ya sa wuraren gurzar audugar wato Ginery da ake da su sun zama ba sa aiki, inda nan ma koma baya ne wajen samar da aikin yi ga matasa.

Daga nan sai ya yi kira ga manoman da ma ‘yan kasuwar da suke safarar audugar cewa su rike harkar da gaskiya domin rashin gaskiya a harkar da yin algus shi ke kara kawo koma baya musamman wajen sayar da ita a kasuwanni domin duk inda a kai auguda ta Gombe ta fi kyau.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *