Mon. Mar 31st, 2025

Sabon Tsarin Harajin Shugaba Tinubu Zai Amfani ‘Yan Arewa -Abdul’azeez Abdul’azeez

By Saleh Aliyu Nov 21, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a kan yaɗa labarai, Malam Abdul’azeez Abdul’azeez, ya bayyana cewa tsohon tsarin da ake a kai na harajin sayayyar kayayyaki da ake kira Value Added Tax (VAT) zai taimaki jihohin Arewa yadda ya kamata.

Ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai, inda ya ce, su kuma sauran jihohi, musamman waɗanda sune ke da mafiya yawan al’umma waɗanda a nan ne aka fi yin hada-hadar sayen kayayyakin, amma saboda ba a nan hedikwatar kamfanoni masu sarrafa kayan suke ba sun zama tamkar an ci yaƙi da su ne, amma ana barin su da kuturun bawa ne kawai wajen amfanar harajin.

Ya kafa misali da cewa jihar Kano abin da take karɓa bai taka kara ya karya ba daga tsarin harajin duk da tana da ɗimbin mutane, amma jihohin Legas, Rivers, Oyo da Ogun da a nan kamfanoni suke sai ka ga su suke ɗaukar kaso mafi tsoka.

AbdulAzeez Abdulazeez ya ce, ko da a watan 10 da ya gabata, jihohi huɗu kaɗai Legas, Ribas da Oyo da babban Birnin Tarayya Abuja su suka kwashe kaso 70 na harajin VAT da aka ƙara a watannin baya.

Abdul’azez Abdul’azez ya ce, don haka ita wannan doka da shugaban ƙasa yake so a gyara yanzu da wasu mutane ba su fahimci amfaninsa ba, abin da ake so a yi shi ne, ya zama ana duba biyan harajin VAT ta duba daga inda kuɗin ya fito, ba wai a ina ne hedikwatar kamfanin da suke zuwa su biya harajin ba.

Ya ce ga misali ana iya samun wani kamfanin sadarwa na waya na da hedikwata a Legas, amma in aka duba nawa mutanen Kano suke kashewa wajen sayen kati na yin waya da layin kamfanin, za a duba wannan yawan adadin ne, a biya masa haraji a bai wa jihar Kano kaso mafi tsoka a ciki ba kamar yaɗda ake yi yanzu ba, saboda kawai hedikwatar kamfani na waje sai su sami kaso mafi tsoka .

Abdul’azez ya ce wannan shi ne sabon tsarin da za a zo da shi, wanda kuma ta yin haka ɗin, za a sami sauƙi matuƙa da gaske, kuma jihohi da suke da mutane da ake hada-hadar sayen kayayyakin mafi yawa su za su sami kaso mafi tsoka a sabon tsarin.

Malam Abdul’azeez Abdula’azeez ya ce, “Tsarin zai amfane mu a Arewa da mune ke da mafi yawan al’umma. Ya kamata ma mu fi kowa son kawo wannan tsarin da zai dawo da kuɗaɗe ga jihohi da ake sayen kayan ba wai ga jihohi da a nan ne hedikwatar kamfanoni da ke samar da kayayyaki suke ba”, in ji shi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *