Daga Ibrahim Muhammad
Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano (AKCOE) da haɗakar Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta gudanar da bukin rantsar da sabbin ɗalibai karo na biyu da za su yi karatun neman digiri na Jami’ar Tarayyar Dutsenma a ƙarƙashin Kwalejin Ilimin ta Aminu Kano da kuma ƙaddamar da kundin littafin bincike (Journal).
An gudanar da taron ne a Kano ranar Lahadi ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban Jami’ar Tarayya na Dutsinma, Farfesa Armiya’u Harisu Bichi, wanda a jawabinsa ya yi kira ga sabbin ɗaliban a kan su jajirce da aiki tuƙuru da tarbiyya wajen yin karatunsu da a ƙarshe za su sami kyakkyawan sakamako da za a yaye su a Jami’ar.
Faresa Armiya’u ya gargaɗi sabbin ɗaliban a kan su guji duk wasu munanan ayyuka da kuma satar jarabawa su ba da kulawa a kan abin da ake koya musu domin samun sakamako mai kyau.
Ya yaba wa irin ƙoƙarin da Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano da suke haɗaka da Jami’ar su wajen bayar da nagartaccen ilimi ga ɗaliban. Sannan ya yaba da matakan da gwamnatin jihar Kano ke ɗauka wajen tallafawa bunƙasa cigaban ilimi.
Shi ma a jawabinsa shugaban Kwalejin Ilimi na Aminu Kano, Dakta Ayuba Ahmad ya ce an yi taro ne domin rantsar da ɗalibai da za su yi karatun digiri na farko da ake yi mazaunin Kwalejin haɗin gwiwa da Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Dutsinma da kuma ƙaddamar da kundin littafi na binciken ilimi da malamai na Jami’a da Kwalejin Ilimi suka haɗu suka wallafa.
Dakta Ayuba Ahmad ya yi nuni da cewa suna samun kyakkyawan shaida na cewa a cikin Kwalejin Ilimi da aka kafa masu tasowa ta Aminu Kano na daga na sawun gaba wajen inganci kuma sune suka soma wallafa wannan kundin bayanai na bincike da aka fi sani da Journal.
Ya ce, “Kwalejin na ba da darussa masu yawa a ɓangaren NCE. Akwai kwasa-kwasai sama da 20. Haka suna darussan Kimiyya da ɓangaren ilimin addini da sauran muhimman darussa. A ɓangaren digiri ma suna gudanar da kwasa-kwasai kamar 10.”
A yayin taron an ƙaddamar da kundin littafin bincike (Journal) na Kwalejin da babban mai ƙaddamarwa Shaikh Dakta Ali Muhammad Barnawi ya ƙaddamar da a kan N1,000,000, shi ma mataimakin Gwamnan jihar Kano, wanda kuma shi ne Kwamishinan ilimi na manyan makarantu Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙaddamar a kan N5,000,000 da sauran mutane da dama da suka bayar da gudunmuwa a yayin ƙaddamarwar.