
Babban sifeton ‘yan sandan, Kayode Egbetokun, ya bayar da chekin Naira biliyan 2.08 ga iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki cikin shekara biyar da suka gabata.
Cikin wata sanarwa da mai magana yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce an bayar da chekin kuɗin ga mutum 785 da za su amfana da kuɗaɗen.
“Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta hanyar ofishin kula da inshora, ya samu damar warware haƙƙoƙin mamata kusan 2,533 wanda ya kama kusan Naira biliyan 6.01 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa yau”, in ji sanarwar.
Kamar yadda BBC ta ruwaito, Babban sifeton ‘yan sandan ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu, saboda sanya walwalar ‘yan sanda cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.
A Nijeriya dai iyalan jami’an tsaro kan shiga tasku bayan mutuwar iyayensu ko mazajensu waɗanda suka sadaukar da rayukansu wajen bauta wa ƙasa.
