Daga Ibrahim Muhammad
An bayyana rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Sanusi Abbas da cewa jihar Kano ta yi babban rashi na Uba, Basarake Jagora.
Hon. Usman Bala ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano.
Ya ce marigayi Abbas Sunusi mutum ne mai juriya da haƙuri da yawan nusar da mutane a kan kyawawan ɗabi’u da za a cigaba da koyi da su.
Alhaji Usman Bala, wanda ɗaya ne daga masu bai wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf shawara na musamman ya ce, tun tasowar su suke jin irin gudummuwa da marigayi Abbas Sanusi yake bayarwa wajen kare kima na masarautar Kano da al’ummar jihar Kano a dukkan muƙamai da ya riƙe a masarautar.
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan ss, ya bai wa al’ummar Kano da gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba
Kabir Yusuf da Sarkin Kano Muhammad Sanusi da sauran iyalai haƙurin jure wannan rashin, tare da addu’ar Allah ya yi masa rahama.
Shi ma a yayin ziyarar ta’aziyyar da ya kai gidan Galadiman Kano, Shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa na jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, rasa dattijo irin Alhaji Abbas Sunusi, babban rashi ne ga jihar Kano da Arewa da ma ƙasa baki ɗaya, idan aka yi la’akari da irin tsawon lokaci da Allah ya bai wa Galadima yana hidimta wa al’umma.
Barista Muhyi Magaji ya yi fatan matasa za su yi koyi da irin nagartattun halaye irin na marigayi Galadiman Kano, Abbas Sanusi domin tabbatar da haɗin kan al’ummar jihar Kano da na ƙasa baki ɗaya.