Mon. Mar 31st, 2025

Rabon Awakin Kiwo Ga Mata: Babu Wani Abin Alheri Da Gwamna Abba Kabir Zai Yi ‘Yan Adawa Ba Su Yi Hamayya Ba -Habib Mailemo

By Saleh Aliyu Jan 26, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa babu wani abu na alheri da za a yi na ci gaban al’umma da gwamnatin Abba Kabir yake yi da ‘yan adawa za su ja baki su yi shiru ba su ce komai ba, sai dai abin da ya gagare su. Abin takaicin shi ne yadda mutane sukan yi maganganu na ƙirƙira da ba su da tashe balle makama.

Shugaban ƙungiyar Proper ta jihar Kano, Hon. Habibu Saleh Muhammad Mailemo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida

Ya ce duk masu surutai na ƙarerayi a kan Gwamnan Kano ya raba tallafin awakai na kiwo ga mata a kan maƙudan kuɗaɗe masu yawa babu wata jarida mai bin ƙa’aida da dokokin aikin da ta ɗauke shi da muhimmanci in ban da wata da ake kira sahara ita dama sukan ɗauki labari ne ba tare da bincike ba.

Ya yi nuni da cewa tsarin rabon awakin da aka yi shi ne na biyu a zuwan gwamnatin Abba Kabir Yusuf a shekarun baya ma lokacin Kwankwaso yana Gwamna an yi irin wannan tsarin na raba awaki da shanu har makaranta aka samar da ake koyar da kiwo, sannan a bai wa wanda suka gama makarantar dabbobi a matsayin wanda ake sa ran su je su riƙe kansu da al’umma.

Ya ƙara da cewa mutane masu hamayya sun faɗi gundarin kuɗi da suke cewa an kashe sama da biliyan biyu, amma ba su bincika sun ga abubuwa da aka haɗa aka bayar da ya shafi kiwon dabbobi ba, wanda a ciki ban da awakai da aka raba akwai shanu da raguna har da tsirrai na harkar rainon fulawowi da yanda ake kasuwancinsu.

Hon. Habib Saleh Muhammad ya ce, “Akuyoyi da aka raba babu wacce gwamnati ta saye ta a sama da N58,000. Sannan kuma masu haihuwa ne a kai a kai. A shekara za su iya haihuwa sai uku. An bayar da kuyoyi biyu da bunsuru ɗaya ga kowace mace, idan bibbiyu suke haifa a shekara za a samu huɗu sau uku kusan 12 ke nan a shekara.

“Sannan bincike da aka yi ya nuna mata da aka bai wa a lokacin Kwankwaso, har yanzu akwai waɗanda suke amfana da ya zame musu kashin bayan haɓakar tattalin arziƙinsu a cikin gida. Da kiwon suke biyan buƙatu da hidimominsu da ka iya tasowa har ma da tallafa wa mazajensu,” ya tabbatar.

Hon. Habibu Saleh Mailemo, wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Fagge ne ya ce, yanzu a ƙasashen duniya da dama harkar kiwo na daga abubuwa da ke bunƙasa tattalin arziƙi. “Kuma idan waɗanda suka amfana suka kiwata dabbobin nan da aka ba su, zuwa shekara ɗaya za su samu haɓɓaka duk shekara za su samu ɗimbin akuyoyi, amma su mutane ba sa duba tunanin gwamnati da manufarta a kan duk abubuwa da take yi wanda ba a zartar da su sai an yi gwaji an ga amfaninsu.

Ya ce su masu adawa ba sa aunawa su ga nawa ne kuɗin sa da aka saya aka bai wa mutum, guda biyu da abincinsu na wata uku, sannan a cikin ɗalibai da aka yaye a kan kiwo akwai wanda aka bai wa kuɗaɗe wannan su suke haɗuwa a irin gudunmuwa da gwamnati take bayarwa.

Sannan ya yi kule da cewa in ban da ma gwamnatin jihar Kano wacce take komai bisa adalci da bin ƙa’ida, wacce gwamnati ce ke fitowa ta bayyana kuɗaɗen da take kashewa kan abubuwa da take aiwatarwa. Wannan ma dama ce da ake bai wa mutane su yi bincike a kai.

Shugaban ƙungiyar Proper na jihar Kano, Hon. Habibi Mailemo ya yi nuni da cewa masu hayagagar an yi zuraren fitar da maƙudan kuɗaɗe, an sayi dabbobi da aka raba wa mata da a kan gaskiya suke da ‘yan jarida sun faɗi abin da suka gani, shi ya sa irin wannan shaci-fadin ɗin da ake ba sa ɓata lokaci don kariya.

Ya ce amma saboda mutane su sani bayan dabbobi akwai raguna ma da za a bai wa maza 15 kowanne guda biyu a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano rago da tunkiya su kiwata domin su amfana.

Ya ce gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf na ƙoƙari ne wajen ganin ta haɓɓaka noman dabbobi da a ɓangare ɗaya, kuma yana taimakawa wajen gyara gonaki da samun kuɗin shiga da samar da kayan abinci da na dabbobi don haka ba sa mamaki idan suka ji wani da ya zo yana ƙarya da baloƙoƙo kan cewa ba a yi abin da zai amfani jama’a saboda masaniyar adawa.

Hon. Habibu Saleh Muhammad Mailemo ya a ce ƙungiyar da yake shugabanta ta Kano Proper a ƙarƙashin tsarin Kwankwasiyya, kamar sauran ayyuka sun tabbatar da ganin bai wa mata guda 35 a kowace ƙaramar hukuma ta Kano dabbobin guda uku duk mace ɗaya kamar yadda aka tanada suna ci gaba da bibiya, kuma na ganin yadda ake kula da su, domin su bai wa gwamnati bayani a kan tasiri da amfanin tsarin da abin da ya kamata a yi a gaba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *