Tue. Apr 1st, 2025

Ogan Ɓoye Ya Nuna Jin Daɗinsa Na Buɗe Rukunin Manyan Shaguna Na Ɗan’aggo A Nasarawa

By Saleh Aliyu Dec 23, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye, ya ce ba za su manta da gudunmawar da babban ɗan kasuwa a jihar Kano, Alhaji Lawwali Ɗan’aggo ya zo ya kafa a yankin ba na gina makeken rukunin shaguna na zamani (Plaza) don bunƙasa harkar kasuwanci a yankin.

Ogan Ɓoye ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a yayin taron bude rukunin shagunan Ɗan’aggo Plaza da Alhaji Lawwali Ɗan’aggo ya gina a yankin.

Ya yi nuni da cewa da ana samun irin wannan daga mutane masu hali da dama da an rage ɗimbin matasa da ba su da aikin yi. Ya roƙin Allah ya ƙaro irin su da yawa a cikin al’umma, musamman a ƙaramar hukuma Nasarawa.

Ogan Ɓoye ya ce ƙaramar hukumar Nasarawa tana da matasa da yawa, buɗe irin waɗannan manyan shuguna zai ba da dama a sami abin yi a cikin ɗan gajeren lokaci ko ba a yi walwal ba, za a yi ƙyalƙyal. “Don haka ya roƙi ‘yan kasuwa da cewa suna da buƙatar irin waɗannan manyan shaguna a yankin don kasuwanci ya haɓɓaka. sannan kuma a samu ƙarin kuɗaɗen shiga a ƙaramar hukumar a yi wa al’umma aiki,” ya bayyana.

Hon. Yusuf Imam ya yi wa Alhaji Lawwali Ɗan’aggo fatan alheri da addu’ar Allah ya yi masa jagora, kuma waɗanda za su shiga katafaren rukunin shagunan na Ɗan’aggo ya sa albarka a kasuwancin da za su yi.

Shi ma tunda farko a jawabinsa na maraba, shugaban rukunin Ɗan’aggo Business Plaza, Alhaji Lawwali Ɗan’aggo ya gode wa Allah da ya ba shi dama ya gina waɗannan rukunin shaguna da suka ƙunshi shaguna guda 620 da za a sayarwa ‘yan kasuwa, musamman masu ƙaramin ƙarfi da kuma ba da hanyarsu a kan farashi mai sauƙi domin taimakawa cigaban kasuwanci a ƙaramar hukumar Nasarawa da jihar Kano gaba ɗaya.

Ya ce shugunan an samar musu da kayan buƙatun da suka haɗa da rijiyar burtsatse da tsarin kula da tsaro mai inganci da kuma tanadin kayan kashe gobara na karta- kwana da duk wani abu da zai kyautata yanayi da tsari na gudanar da harkokin kasuwanci cikin walwala.

Alhaji Lawwali ya gode wa shugabanni da iyayen ƙasa da jagororin addini da ‘yan kasuwa manya da ƙanana da sauran al’umma da suka amsa gayyatarsa ta zuwa buɗe katafaren rukunin shagunan na kasuwancin na Ɗan’aggo.

Shi ma da yake jawabi a madadin abokan Ɗan’aggo Alhaji Abdulrazaƙ Salisu da aka fi sani da Tsanyawa, wanda shi ne mai ba da shawara a kan ginin rukunin shagunan kasuwancin na Ɗan’aggo, ya ce, “Wannan rana ce ta farin ciki a gare mu, sakamakon amininmu abokin mu’amalarmu da Allah ya ba shi iko ya gina katafaren Plaza. Muna daga cikin jiga-jigan da muke sayar da shagunan ciki da bayar da hayarsu,” ya tabbatar.

Ya ce dama an yi babban ginin shugunan na Ɗan’aggo ne domin sayarwa da sanya haya ga ‘yan kasuwa. Ya ce, “Muna fata Allah ya ƙaro ‘yan kasuwa a jihar Kano irin su Alhaji Lawwali su zo su ɗauki irin wannan salo domin ƙara ɗaukaka Kano.”

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *