Wed. Apr 2nd, 2025

NDLEA Ta Kai Samame Sansanonin Hada-Hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano

By Saleh Aliyu Dec 25, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta ƙasa reshen jihar Kano, ta yi nasarar daƙile hada-hadar ƙwayoyi da sauran kayan maye a faɗin jihar Kano.

Mai magana da yawun Hukumar na jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema Larabai.


Ya ce sun sami wannan nasarar ne sakamakon baza jami’an hukumar da aka yi a dukkan inda ake zargin mafaka ce ta masu dillacin miyagun ƙwayoyi.

Sanarwar ta ce a ranar Talata babban Kwamandan hukumar na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya baza jami’an hukumar domin daƙile hada-hadar dukkan wasu kayan maye a lungu da saƙo na jihar, duba da yadda aka saba yi a lokacin bukukuwa.

Ya ce wuraren da aka kai sumamen sun haɗa da cikin Fagge, filin wasa na Sani Abacha da kuma unguwar Ɗan Agundi, har aka sami nasarar kama mutane 34 a waɗancan wurare.

Sanarwar ta ƙara da cewa matakin hukumar ya haifar da kyakkyawan sakamako da yanzu haka an fara tantance waɗanda aka kama domin a gurfanar da dillalan a gaban kotu, su kuma masu shan kayan mayen a ba su taimakon da ya dace.

Hukumar ta NDLEA ta buƙaci al’ummar jihar Kano su cigaba da ba su cikakken haɗin kai da goyon baya, domin a sami nasarar fatattakar masu yin ta’ammuli da kayan maye a jihar.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *