Tue. Apr 1st, 2025

Na Ji Daɗin Cika Burin Mahaifina Na Gina Masallaci Da Makaranta Da Na Yi -Aminu Umar Mai Famfo

By Saleh Aliyu Jan 5, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci ƙaddamar da buɗe makaranta da masallaci wanda mataimakin manajan daraktan Hukumar KASCO, Hon. Aminu Aminu ya gyara aka ƙaddamar a matsayin khumusi da wakafi ga mahaifinsu marigayi Aminu Umar Mai Famfo a Unguwar Kawaji.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddamar da buɗe makarantar, Hon. Aminu Aminu Mai Famfo ya ce dama makarantar da masallacin harsashi ne da mahaifinsa ya dasa bayan ya rasuwarsa cikin ikon Allah bayan shekara 20 ya tabbatar da wannan niyya na mahaifinsa ya gyara makarantar da masallacin domin cika masa niyyar tasa.

Ya ce gode wa Allah da ƙaddamar da buɗe makaranta da masallacin da cika wa mahaifinsu niyya na tabbatar da wannan makaranta a matsayin kyauta da kuma saka ta a matsayin Waƙafi ga mahaifin nasu.

Hon. Aminu Aminu Mai Famfo ya ce sun kafa kwamiti da za su kula da makarantar tare da damƙa ta a hannun gwamnatin jihar Kano domin mutane su sami sauƙin yin karatu kyauta a makarantar.

Sannan suna da shirin samar da Islamiyya da ƙirƙiro hanyoyi da za a taimaka wa ɗalibai koyon yin sana’o’i na hannu, kuma za su cigaba da bayar da duk wata gudunmuwa a gwamnatance da kuma nasu nakan su domin cigaban makarantar.

Hon. Aminu Aminu Mai Famfo ya ce yana cikin matuƙar farin ciki na cika wa mahaifinsa wannan niyya da alƙawari, domin duk wani da yake so ya tabbatar cewa ya zama ɗa nagari wajen yin abin alheri ga iyayensa ya gode wa Allah da wannan dama da ya ba shi na cika wannan niyya.

Hon. Aminu Aminu ya yi kira da cewa ya kamata mutane su riƙa ɗaukar irin wannan ayyuka ya zama abin koyi, kuma duk lokacin da kake tasowa kake manyanta ka riƙa yin abin da na baya za su riƙa amfana na alkhairi. “Don haka matasa su ɗauki hanyoyi da zai sa a sa masu albarka da kyautatawa rayuwar al’umma,” ya ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *