Inji-Algon President
Daga Zubairu M. Lawal Lafia
Samarwa Sarakuna da gulbin aiki a tsarin mulki zai kara tabbatar da zaman lafiya a tarayyar Nijariya.
Shugaban Chiyamomin Nijariya (Algon president) kuma Shugaban karamar Hukumar Lafia Alhaji Aminu Ma’azu Maifata ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Lafia.
Aminu Ma’azu Maifata yace; tun ina mataimakin Shugaban Chayamomi na kasa nake bada shawarar shigor da Sarakuna cikin tsarin Gwamnatin Qasa.
A yanzu da na zama Shugaban Chayamomi na kasa wato (Algon president) na taso da wannan kuddurin, saboda ina da tabbacin Sarakuna suna da rawar da zasu taka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Dan hakane nake da burin ganin cewa an Samar masu da gurbi cikin Gwamnati.domin gudanar da aikin da zai hada kan al’umma da tabbatar da zaman lafiya.
Yace; duk Shugaban karamar Hukumar yana fatan yaga an tabbatar da wannan kuddurin saboda Sarakuna suna taimakawa Shugabannin kananan Hukumomi da shawarwari na cigaba a kowani vangare. Masamman idan ana bukatar zaman lafiya.
Maifata yace; a ranar Asabar a jihar Nasarawa kowa yaga yadda sarakuna suka nuna hadinkai sun dunkule waje guda a bikin murnar cika shakaru biyar na Sarkin Lafia kan gadon mulki.
Babu sassa a fadin kasan nan da Sarakuna basu zoba. Aminu Ma’azu Maifata ya yaba da salon Sarautan Mai Shari’a Sidi Bage.
Yace; Shekara biyar da Mai Shari’a Sidi Bage Muhammad yayi kan gadon Sarautan Lafia an samu cigaba sosai.
Lokacin da aka zaveshi a matsayin Sarki ina Shugaban karamar Hukuman Lafia.
An gudanar da zave babu musgunawa babu tilastawa saboda Gwamnati batada Dan takara tabar masu zaven Sarki su zabe Wanda sukeso.
Wadanda suka zabe sarkin sun roke Gwamnati kada ta chanza masu Wanda suka zabe.
Ko da yahau kaujerar mulki bai baiwa jama’a kunya ba. Abinda ake tsamnani na tabbatar da zaman lafiya da cigaba an gani a gareshi.
Ya hada kan al’umman Lafia kowata qabela bako da yan gari, kowa na yabon Sarki Sidi Bage.
A matsayina na Shugaban karamar Hukumar Lafia, ina jin dadin zama da Sarki Sidi Bage. Saboda duk da matsayinshi na Uba a gareni Amma duk inda zai yi tafiya cikin jihar ko wajen jihar sai ya sanar da ni. Idan nace ai wannan babu damuwa sai yace a’a ai dokane tace haka. Shi kuma mai bin dokane.
Kuma duk abinda zamuyi da ya shafi cigaban karamar Hukumar Lafia zaka tarar dashi ya shigo shine gaba-gaba
Hakama baya wasa da batun maganar zaman lafiya , yana hada kan Hakimai da Dakkatai da masu Unguwanni da masu fada aji. Kai har ranar dokar tsaftar muhalli na karshe wata Sarki na zaga gari ya tabbatar jama’a sun tsaftace muhallinsu.
Hata yan kasuwanmu na garin Lafia da masu koyon Sana’a Sarkin na kokari yaga cigabansu. Yanzu haka Sarki yayi kokari an kawo mana makarantar koyon Sana’a. a karamar Hukumar Lafia an kawo kayayaki komai da komai. mukuma Qaramar Hukumar munba da fili ana ginawa a Akunza,
Daga karshe (Algon President) yayi kira ga al’umman Qaramar Hukumar Lafia dasu cigaba da adu’o’i na alheri ga Sarkin Lafia Mai shari’a Sidi Bage.
Ya kuma yikira ga al’umman jihar Nasarawa da su cigaba da baiwa Gwamna Abdullahi Sule goyon baya domin cigaban jihar Nasarawa.
Yace; dole al’umman jihar Nasarawa su yabawa Gwamnatin Abdullahi Sule saboda ayyukan alheri da yake gudanarwa a kowata karamar Hukumar da Lafia babban birnin jihar.
Hoto
Shugaban Chiyamomin Nijariya (Algon president) kuma Shugaban karamar Hukumar Lafia Alhaji Aminu Ma’azu Maifata