Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano, Kwamared Babangida Musa, ya bayyana mutuƙar farin cikinsa game da matakin da Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf yake ɗauka na biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu wanda a baya aka daɗe ba a biya.
Ya ce su shaida ne a baya yadda ake ta gwagwarmayar a biya ‘yan fansho har ana fitowa zanga-zanga da har wasu su faɗuwa su mutu, amma yau ga shi cikin murna da farin ciki mutane da suka gama aiki suka ɗauki dogon lokaci suka yi ritaya ana biyan su ba tare da tayar da jijiyar wuya ba.
Ya ƙara da cewa, “Babu abin da za mu ce wa Gwamna Abba Kabir sai dai Allah ya saka da alheri, ya yi riƙo da hannayensa. Kullum abin da ya shafi haƙƙin talakawa da ma’aikata yana iya bakin ƙoƙari domin sauke nauyi da Allah ya ɗora masa.”
Ya yi nuni da cewa kwanan nan Gwamna ya biya ma’aikata mafi ƙarancin albashi na ₦71,000, wanda jihohin da suke Arewa maso Yamma ba su biya ba. Don haka ya ja hankalin ma’aikata su tsaya su riƙe aikinsu da kyau domin su tallafa wa wannan gwamnati domin tana sauke nauyin ta.
Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiyar na jihar Kano ya ce su ma su so su bar manufa mai kyakkyawa a wannan ƙungiya da yake shugabanta kamar yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf take jajircewa. “Haka mu ma mu jajirce mu tallafawa manufar gwamnatin Kano a kan inganta lafiya,” ya jaddada.
Kwamared Babangida Musa shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ma’aikatan lafiya na jihar Kano, ya ce a baya ana samun yin sakaci da aiki sakamakon yadda gwamnatin da ta gabata ba ta ba da kulawa ga ma’aikatan, amma zuwan wannan gwamnati a tsaye take a kan kula da haƙƙoƙinsu, su kuma a ƙungiyance za su tsaya su tabbatar ma’aikata sun yi abin da ya kamata, domin ci gaban harkar lafiya a jihar Kano.