Thu. Apr 3rd, 2025

Muna Fuskantar Babbar Barazana -Masu Sana’a A Babbar Kasuwar Rano, Kano

By Saleh Aliyu Feb 7, 2025

Daga Ibrahim Muhammad Kano

‘Yan kasuwa a babbar kasuwar garin Rano da ke jihar Kano, sun nuna matuƙar damuwarsu a kan matakin da shugaban ƙaramar hukumar ke shirin ɗauka na rushe kasuwar gaba ɗaya a sake mata sabon fasali. Suna fargabar hakan zai jefa su cikin matsala.

Majiya mai tushe ta shaida mana cewa, shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon. Naziru Ya’u ne ya nemi ‘yan kasuwar su tashi domin ya gayyato wani kamfani zai yi wa kasuwar gini na zamani, sannan a sayar wa ‘yan kasuwa runfunan.

Hakan ta sa mazauna kasuwar da ta kafu kusan shekaru 100 suke gudanar da harkokin kasuwarnci a ciki hankalinsu ya tashi, domin mafi yawa ba za su iya sake mallakar wajen ba idan an gina.

‘Yan kasuwar sun kai kokensu ga shugaban ƙaramar hukumar Nasiru Ya’u, amma ya ce babu gudu, babu ja da baya a shirinsa na rushe kasuwar da gina sabuwa. Don haka ma ‘yan kasuwar suka kai koke ga Sarkin Rano da sauran masu ruwa da tsaki a yankin a kan a ja hankalin shugaban domin kar ya jefa su a yanayi mara dadi, amma ya kafe a kai.

‘Yan kasuwar sun yi nuni da cewa gina irin wannnan kasuwar ko a cikin birni ba kowa ne yake da ƙarfin mallakar rumfa ba bare a karkara da ɗan kasuwa yake ɗan juya jarinsa, idan aka zo aka karbe musu runfuna aka gina sabbi, sai a sa miliyoyin kuɗi da ba za su iya saya ba.

“In an duba irin sana’ar da muke yi, ba mu kai ƙiyasin da za mu iya sayen runfunan ba. Sannan waɗanda suke da runfunan tun na gado ba na gwamnati ba, ba su da kuɗin da za su iya mallaka,” in ji wani ɗan kasuwar da ya nemi a saka sunansa.

Mun tuntuɓi shugaban kasuwar Alhaji Alkasim Hamza ya tabbatar mana da cewa tabbas shugaban ƙaramar hukumar Hon. Nasiru Ya’u ya ce ba gudu, babu ja da baya a wannan manufa tasa ta rushe kasuwar da tun iyaye da kakanni suke a wajen.

Ya ce hatta wanda yake cikin rumfar gwamnati ba za a biya shi diyya in an rushe masa, ya za a sake yi idan an gina?

Ya ce sun koka wa shugaban ƙaramar hukumar ta gaba da gaba da ta rubuta masa takardu har ya kirawo wakilan ‘yan kasuwar ya zauna da su a gaban DSS, amma daga baya ya ce babu wanda ya isa ya hana shi ya rushe.

Alhaji Alƙasim Hamza a madadin ‘yan kasuwar sun yi kira ga Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a tausayi da adalcinsa ya sa musu baki a wannan lamari kar a tashe su daga inda suka gada iyaye da kakanni suke kasuwanci.

“Domin mafi yawan ‘yan kasuwar ba za su iya mallakar wajen ba idan an gina. Suna ganin zai fi dacewa shugaban ƙaramar hukumar ya nemi wani filin na daban ya gina sabuwar kasuwa ta zamani mai iko da halin saye sai ya saya,” in ji shi.

Alhaji Alkasim Hamza Rano ya ce ba suna jayayya ga shugaban ƙaramar hukumar bane, suna dai kira gare shi ne a yi musu adalci, a yi la’akari da yanayi da halin da ake a ciki a tausaya musu kar a jefa su a halin rashin jin daɗi.

Duk ƙoƙarin da muka yi don ji daga bakin shugaban ƙaramar hukumar Rano Hon. Naziru Ya’u, abin ya ci tura.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *