Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Rimin Gado a jihar Kano, Hon. Sani Salisu, ya bayyana ɗan majalisar jiha mai wakilatar Rimin Gado da Tofa a majalisar dokokin jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Butubutu da cewa shugaba ne abin koyi. “Duk wanda yake shugabanci zai so ya yi koyi da halayensa nagari.”
Ya ce, “Duk wanda ya san shi ba abin da zai faɗa maka sai halayensa na kirki. Ba a Rimin Gado da Tofa kaɗai ba, hatta a jihar Kano baki ɗaya wanda ya san shi, zai gaya maka mutumin kirki ne mai magana ɗaya. Idan ka je gidansa a ranekun ƙarshen mako za ka sami sama da mutum 100 maza da mata ba sai in ana taro ba, waɗanda talakawa ne daga yankunan ƙananan hukumomin da yake wakilta su kawo kokensu da matsalolinsu.
Ya ce a tarihin Rimin Gado da Tofa ba a taɓa samun ɗan majalisar jiha ba da ya je majalisa a jere sau uku sai a kan Hon. Muhammad Bello Butubutu aka fara saboda amincewa da shi da al’umma suka yi da irin ayyukan alkhairi da mu’amala da talakawansa da yake.
Hon. Sani Salisu ya yi nuni da cewa don haka shi ma da ya koyi siyasa daga gare shi a matsayinsa na jagoransu, ga shi Allah ya sa ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, kuma za su cigaba da koyi da shi a siyasa. “Muna da tsare-tsaren gudanar da muhimman ayyuka na cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Rimi Gado,” in ji shi.
Shugaban ƙaramar hukumar na Rimin Gado Hon. Sani Salisu ya ce a cikin wata ɗaya da ya soma jan ragamar shugabanci sun tsara da kawo abubuwa na cigaba da haɗin kai da mutunta juna da soma samawa yara makarantu na ɓangaren kula da lafiya. “Sannan mun shirya yin ayyuka da yawa da za su kawo wa ƙaramar hukumar ci gaba cikin yardar Allah,” ya ƙarƙare.