
Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana nadama kan yadda yankin ya zabi Shugaba Bola Tinubu a 2023.
A wata hira da jaridar GUARDIAN a ranar Talata, Abdul-Azeez Suleiman, mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa (NEF), ya ce sun yi nadamar zaben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, amma sun koyi darasi daga kuskuren da suka aikata.
“Arewa ta yi kuskure wajen zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023, kuma da wuya su sake maimaita kuskuren nan gaba.
“Sun koyi darasi daga kuskuren da suka yi a baya kuma za su yi kokarin zabo dan takarar da zai iya hada kan kasar nan tare da gudanar da mulki domin amfanin ‘yan Najeriya baki daya.
“Arewa za ta yi taka-tsantsan wajen zabar dan takarar shugaban kasa. Za su ba da fifiko ga wanda ake ganin ya fi kowa cancanta, wanda ba ya jawo cece-kuce, kuma ya fi dacewa da muradun daukacin yankunan kasar.
“Kuskuren da muka yi na goyon bayan Tinubu a 2023, ya koya mana darasin sanin mahimmancin hadin kai da fahimtar juna wajen zabar dan takara mafi girma a kasar,” in ji shi.
A cikin ’yan takara uku da ke kan gaba a zaben shugaban kasa na 2023, Bola Tinubu, wanda ya tsaya takara a jam’iyyar APC, shi ya fi samun yawan kuri’u daga yankin Arewa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu dai na sha suka sosai kan wasu manufofin gwamnatinsa, wadanda suke kara jefa rayuwar jama’a cikin kunci.
A farkon makon nan ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, babban mai kalubalantar Tinubu a zaben shekarar da ta gabata, ya ce manufofin shugaban kasar babu jinkai da tausayi a cikinsu.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar dangane da karin kudin wutar lantarki.
Sai dai kuma shugaban ya sha ba ’yan Nijeriya tabbacin cewa ranaku mafi muni sun wuce, yana mai cewa gwamnatinsa ta shawo kan matsalolin da jama’a ke fuskanta.
Bayan rattaba hannu kan kudirin lamunin dalibai a makon da ya gabata, Tinubu ya ce makomar yaran Najeriya za ta yi haske domin an kama hanyar fitar da su daga kangin talauci.
Ya kuma ce tattalin arzikin kasar na kara murmurewa daga halin da ya fada, kuma ana daukar matakin magance hauhawar farashin kayayyaki.
“Abin da kawai zai iya yaki da talauci shi ne ilimi. A yau, na sanya hannu kan tsarin lamuni na dalibai. Ka yi tunanin ’ya’yan talakawa. Ta yaya za ku gaya wa ‘ya’yansu cewa makomarsu za ta yi haske? Ta hanyar ilimi ne za mu iya yakar talauci. Kyakkyawan makoma tana jiran yaranmu,” in ji shugaban a wajen liyafar cin abincin dare a Aso Rock.