Daga Ibrahim Muhammad
Kansila mai wakiltar Mazaɓar Fagge C a majalisar kansiloli na ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Sanusi Sharif Kantoma, ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar Hon. Salisu Usman Masu, bisa irin tagomashi da tausayi da sanin ya kamata da ya nuna ta hanyar ƙara wa ma’aikatan wucin-gadi na yankin albashi.
Kansilan, wanda shi ne shugaban kwamitin da shugaban ƙaramar hukumar ya naɗa domin tantance yawan adadin ma’aikatan wucin-gadi a yankin na haƙiƙa da biyansu sabon albashin ya ce, wannan mataki da shugaba ƙaramar hukumar ya ɗauka ba ƙaramin abin alheri ba ne da daɗaɗa wa ma’aikatan.
Hon. Sanusi Shariff Kamtoma ya ce, wannan aiki da shugaban ya ɗorawa kwamitin da ya jagoranta sun yi aiki tuƙuru bisa gaskiya da amana. Sun shiga dukkan assan ma’aikata na ƙaramar hukumar sun yi bincike na ƙwaƙwaf sun gano cewa daga ma’aikatan da ake da su 300 na wucin-gadi da ake biya a baya, guda 101 ne halastattatu na gaskiya duk sauran cushe ne.
Sanusi Kantoma ya ƙara da cewa bayan miƙa wa shugaban ƙaramar hukumar sakamakon rahoton ne sai ya sahale da ƙara wa ma’aikatan da aka tantance albashi daga abin da ake biyansu a baya da bai wuce ₦2,500 ba zuwa ₦10,000, wanda aka ƙaddamar ake biyansu a halin yanzu.
Kansilan na Mazaɓar Fagge C. Hon. Sanusi Shariff Kantoma, ya yi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar da ma’aikata su cigaba da bai wa shugaban ƙaramar hukumar. Hon. Salisu Usman Masu da mataimakinsa da sakatare da daraktan mulki da ‘yan majalisarsa na kansiloli da dukkan masu ruwa da tsaki haɗin kai da goyon baya domin cigaba da amfana da ayyukan da suka yi alƙawarin samarwa.